Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙudiri aniyar rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar horaswa. Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a fadar Élysée, inda ya ce horaswa da ilimi suna da mahimmanci wajen bunkasa ƙasa.
Tinubu ya kuma yi kira ga masu zuba jari daga Faransa da su yi amfani da damar tattalin arziƙin Nijeriya, musamman wajen samar da abinci da harkar sinadaran ma’adinai. Ya ce,
“Ƙofar Nijeriya a buɗe take ga kasuwanci, kuma muna da matasa masu ƙarfi da sha’awar koyo da kirkire-kirkire.”
- Tinubu Zai Tafi Faransa Don Ziyarar Aiki Ta Kwana Uku A Gobe Laraba
- Tinubu Ya Taya Atiku Abubakar Murnar Cika Shekaru 78
Macron ya yaba wa Tinubu kan shugabancinsa mai hangen nesa, yana mai cewa Faransa za ta ci gaba da ƙarfafa hulɗar kasuwanci da Nijeriya, musamman a ɓangaren bunƙasa matasa da masana’antu. Shugabannin biyu sun yi alƙawarin yin aiki tare domin magance ƙalubale na duniya da inganta tsaro a yankin ECOWAS.