Kasar Sin na shirin gina wani sabon zango na tsarin ba da jagorancin taswira na BeiDou, wanda zai kunshi karin fasahohin zamani masu inganci, da samar da hidimomi masu karko da karfi, da sauran manyan hidimomi da suka shafi fannin.
Ana sa ran harba sabbin taurarin dan Adam 3, masu nasaba da wannan aiki wajen shekarar 2027, kafin daga bisani a dora hidimomin sadarwa kansu wajen shekarar 2029, a kuma kammala aikin baki daya zuwa shekarar 2035.
- Nijeriya Ta Shirya Magance Matsalar Almajirai – Tinubu Ga Macron
- Dokokin Gyaran Haraji Sun Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
Sin na fatan cimma bunkasa muhimman fasahohi da dama nan zuwa shekarar 2025, kamar yadda rahoton da aka fitar a Alhamis din nan, a wajen wani taron karawa juna sani, albarkacin ciki shekaru 30 da kafa tsarin ba da jagorancin taswira na BeiDou ya nuna.
A cewar ofishin lura da ayyukan sadarwar taurarin dan Adam na kasar Sin, sabon zangon ba da hidimar na BeiDou, zai rika samar da bayanai na nan take, kuma masu matukar inganci, da dacewa da wuri, da lokaci bisa matsayin koli na tabbaci, har zuwa mizanin mitoci da decimeter.
Kaza lika, tsarin zai rika samar da cikakkun hidimomi masu karade dukkanin na’urori na masu aiki da shi, tun daga doron duniyar bil Adama har zuwa wurare masu nisa a sararin samaniya.  (Saminu Alhassan)