Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci kungiyoyin ’yan kasuwa da masu samar da kayayyaki su yi aiki a matsayin gadoji ga jam’iyyar kwaminis ta CPC da kuma gwamnati ta hanyar ci gaba da yin alaka ta kud-da-kud da manoma, kana su kara himma wajen bude sabon babi a bangaren cimma burin bunkasa gamayyar kungiyoyin masu samar da kayayyaki da ’yan kasuwa.
Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban hukumar soji ta tsakiya, ya yi bayanin haka ne a wani umarni da ya bayar a bikin cika shekaru 70 da kafuwar Gamayyar Kungiyoyin Masu Samar da Kayayyaki da ’Yan Kasuwa ta Kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)