Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi kira ga Sanatocin Arewa da su ki amincewa da ƙudirin gyaran tsarin haraji na Shugaba Bola Tinubu. Ya gargadi cewa amincewa da ƙudirin zai yi mummunar illa ga tattalin arziƙin Arewa da wasu yankuna na Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas.
- Zulum Ya Gabatar Da Ƙarin Kasafin Kuɗi Naira Biliyan 61 Ga Majalisar Borno
- Nijeriya Ta Shirya Magance Matsalar Almajirai – Tinubu Ga Macron
Zulum ya bayyana wa BBC Hausa cewa ƙudirin ya fi fifita Jihar Legas a kan sauran jihohi. Ya ce,
“Ba mu adawa da kudirin domin tsayayya wa shugaban ƙasa ba, sai dai domin kare makomar jihohinmu.”
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake gaggawar amincewa da ƙudirin, saɓanin dokar masana’antar mai da ta ɗauki shekaru 20 kafin amincewa.
Ya ƙara da cewa rashin tuntubar masu ruwa da tsaki ya ƙara janyo matsaloli kan ƙudirin.
“Idan an amince da wannan ƙudirin, nan da shekaru ba za mu iya biyan albashi ba. Dole mu kalli makomar yara da jihohinmu,” in ji Zulum.
Ya yi kira ga shugabanni da su sake duba lokaci da tsarin ƙudiri tare da tabbatar da cewa an yi nazari mai kyau kafin ɗaukar matakin ƙarshe.