Yayin da babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja na kasar, Xi Jinping, ya ba da umarni mai muhimmanci game da binciken ka’ida da aikin gina Makisanci a sabon zamani a kwanan nan, inda ya bayyana cewa, binciken ka’ida da aikin gina Makisanci shi ne babban aikin gina ka’idojin jam’iyyar kwaminis ta Sin bisa manyan tsare-tsare.
A cikin shekaru 20 da suka gabata, aikin nan ya dade yana samar da sakamakon bincike masu inganci da yawa, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yin nazari da bincike da kuma yada sabbin ka’idojin jam’iyyar da kuma tabbatar da matsayin jagora na Makisanci a fagen akida da sauransu a sabon zamani.
Xi Jinping ya jaddada cewa, a cikin sabon zamani da sabuwar tafiya, dole ne a samu gindin zama a kasar Sin, da ci gaba da raya al’adun gargajiyar kasar Sin, da aza harsashi mai inganci na ilmi, ta yadda za a ba da babbar gudummawa wajen inganta Makisanci mai salon zamanintarwa irin na Sin. (Safiyah Ma)