Ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a yankin Latin Amurka, tare da halartar taron shugabannin tattalin arzikin kungiyar APEC da taron kolin G20 da aka gudanar, ya da jawo hankalin kasa da kasa. Yayin ziyararsa, Xi Jinping tare da takwararsa ta kasar Peru Dina Boluarte sun halarci bikin kaddamar da tashar ruwa ta Chancay ta Peru ta kafar dibiyo, inda aka shaida yadda aka tabbatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” a kasar Peru, da ma yadda kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka da sauran kasashe.
Ba wannan ziyara kadai ke iya bayyana sahihancin kasar Sin a wajen aiwatar da harkokin diplomasiyya ba. Tabbatar da ayyuka 8 na inganta raya shawarar “ziri daya da hanya daya” da tabbatar da manyan ayyuka 10 na hadin gwiwar Sin da Afirka wajen zamanintar da kansu, da kuma tabbatar da ayyuka 8 na karfafa raya duniya baki daya da sauransu, mun iya gano cewa, shugaba Xi Jinping ya sha ambata “tabbatar da ayyuka” a cikin jawaban da ya gabatar a tarukan duniya. Sin tana nacewa ga daukar ainihin matakai don tabbatar da hadin gwiwar cin moriyar juna. Alal misali, a karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, kamfanoni Sin sun taimakawa kasashen Afirka wajen gina layin dogo da tsawonsa ya kai kilomita dubu 10 da hanyoyin mota masu nisan kilomita dubu 100. Layin dogo da ke tsakanin Mombassa da Nairobi na Kenya, da kuma layin dogo dake tsakanin Habasha da Djibouti, kana da layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna na Najeriya da dai sauran ayyukan da kamfanonin Sin suka ba da taimakon gina su, na taimaka wa kasashen Afirka wajen kafa tsarin layukan dogo. Bayan wannan, bikin baje kolin kayayyakin da Sin ke shigowa da su daga ketare wato CIIE ya samar wa kamfanonin kasa da kasa damar shiga kasuwannin kasar Sin, don more damammaki da moriyar tsarin dunkulewar duniya baki daya. Kazalika, asusun raya duniya da hadin gwiwar kasashe masu tasowa ya samar wa ayyuka fiye da 150 tallafi.
Kyan alkawari cikawa, yadda kasar Sin ke yi ke nan a wajen aiwatar da harkokin diplomasiyya da kasa da kasa, wanda hakan ya zama alamar da ta yi shuhura da ita a wannan bangare. Hakan ya sa Sin ta samu karin amincewa daga kasashen duniya, har ta karfafa kwarin gwiwa da hadin kai a tsakanin kasa da kasa wajen gina kyakkyawar makomar duniya. (Mai zane da rubutu: MINA)