A jiya Alhamis ne mahukuntan kasar Sin suka sanar da wasu tsare-tsare na fadada kasuwancin fasahohin zamani a yayin da kasar ke kara matsa kaimin bunkasa gyare-gyaren sassa daban-daban da kuma bullo da sabon ci gaba.
A cewar wasu takardun bayanai da ofishin gudanar da al’amura na Kwamitin Tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis da Majalisar Kula da Kasa ya fitar domin fahimtar da jama’a game da sabon yunkurin, kasar tana sa ran kason kasuwancin bangaren gudanar da hidindimu na zamani a cikin daukacin cinikayyar gudanar da hidindimu da ake samu ya zarce kashi 45 cikin dari a shekarar 2029 sannan ya karu zuwa kashi 50 cikin dari a shekarar 2035.
- An Fitar Da Jigo Da Tambarin Shirye-Shiryen Murnar Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa na CMG Na 2025
- Zulum Ya Yi Kira Ga Sanatocin Arewa Da Su Ƙi Yarda Da Sabon Tsarin Haraji
Zuwa shekarar 2035 kuwa, za a kafa ingantaccen amintaccen tsarin gudanar da kasuwanci na zamani mai samun habaka tare da dabbaka cikakken ci gaba a fannin bude kofa na gwamnati, kamar yadda takardun bayanan suka bayyana.
Bugu da kari, takardun sun ce za a kuma yi wani kokari na bunkasa kasuwancin kayayyakin zamani da na fasahohi da ake kerawa da inganta kasuwancin gudanar da hidindimu a zamanance, da daukaka ci gaban kasuwancin odar kaya na zamani da kuma karfafa ci gaban cibiyoyin kasuwancin zamani.
Domin fadada bude kofar gwamnati a bangaren kasuwancin zamani, kasar Sin za ta kara saukaka hanyoyin shiga kasuwa da karfafa zuba jarin waje a bangaren fasahohin zamani. Inda ta hakan za a kara fadada bude bangarorin sadarwar wayoyin salula da na intanet da aladu da sauransu cikin tsari.(Abdulrazaq Yahuza Jere)