Malamai sun yi sabani cikin adadin yawan Matan Manzon Allah SAW, amma dukkansu sun tafi cewa, Matan Manzon Allah SAW, su 11 ne.
Guda shida, Kuraishawa, su ne: Sayyada Khadijadatu bintu Kuwailidu da A’ishatu bintu Ababakrin da Hafsatu bintu Umar da Ummu Habiba bintu Abi Sufyan (‘yar sarkin Makkah) da Ummu Salamata bintu Abi Umayyata da Saudatu bintu Zam’ata.
- Dabarun Kasar Sin Na Kiyaye Yankuna Masu Dausayi Ga Zuriyoyi Dake Tafe
- LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci
Sai guda Hudu, dangin Larabawa, su ne: Zainabu Bintu Jahshin (Banu Asad, ‘yar kuzaimata) da Maimunatu bintul Harisil kilaliyya da Zainabu bintu Kuzaimatul kilaliyya (Ummul Masakin) da Juwairiyyatu bintul Haris. Wadannan hudu, dukkansu dangin Larabawa ne, sai ta Karshe daga dangin Yahudawa, ita ce Safiyyatu bintu Huyai daga Banin Nazir. Wata rana Sayyada A’isha ta taba ce mata (a cikin halinsu na mata), ‘Bayahudiya kawai, baki da komai’ Sai Sayyada Safiyya ta kawo kara wurin Annabi SAW kan abin da Sayyada A’isha ta fada mata, sai SAW ya ce, “je ki ce mata, ke ‘yar uwar Annabi Musa da Haruna ce” don haka waye kamar ki.
Akwai mata guda biyu da suka riga Annabi SAW rasuwa, su ne: Sayyada Khadijah da Zainabu Ummul Masakin. Don haka, Annabi SAW ya rasu ya bar Mata Tara.
An ruwaito cewa Annabi SAW bayan wadannan 11, ya auri wasu kuma 12 amma sun rabu, su ne: Ta farko, Ummu Shuraifin (ita ce wacce ta ba wa Annabi SAW Kanta), Allah Ubangiji tabaraka wa ta’ala ya ce, Ya Rasulallahi in mace ta zo ta ce ta ba ka kanta, to ni ma na ba ka, Annabi SAW ya sake ta kafin tarewa da ita, daga nan ba ta sake aure ba har ta koma ga Ubangiji. Don haka za ta tashi cikin Matan Manzon Allah SAW.
Ta biyu, Urwatu bin Zubairu ya ce ita ce Haulatu bintu Hakeem, tana daga cikin Matan da suka ba wa Annabi Kansu, ta Uku, akwai Kaulatu bintul Kudaibi; ita kuma daga wani gari aka auro ta me nisa, kafin ta iso garin Annabi SAW, Allah Ya amsa rayuwarta, ta Hudu, akwai Amratu bintul yazid; ita wannan Annabi SAW ya sake ta ne.
Ta Biyar, akwai Asma’u bintu Nu’umanal Kindiyyatu; Annabi SAW ya aureta, yayin da ya neme ta sai ta ce “A’uzu billahi minka”, ma’ana ina neman tsarin Allah daga gare ka sai Annabi SAW ya ce mata kin nemi tsari daga wanda ake neman tsari da shi, tafi na sake ki, sai Manzon Allah SAW ya maida ita ga danginta, daga nan ta fara kiran kanta da “shakiyya”. Kila ana cewa, ta hadu da makircin kishiyoyi ne sabida wata hikaya da ake kawowa, cewa, a al’adar mata in an kawo su gidan miji, akan yi musu kwalliya, kila Sayyada A’isha ke yi mata kitso wata kuma cikin Matan Annabi na yi mata kunshi, sai Asma’u tai tambaya da cewa, wace kalma ce Maigida ya fi so ne? Sayyada A’isha ta ce na sani! In ya kira ki, ki ce masa ‘A’uzu billahi minka’ zai kara son ki ma. Annabi SAW ya ji kunyar Allah, a ce a nemi tsari da shi kuma ya saba, shi ya sa ya ce to tafi gida.
Ta Shida, Akwai Mulaikatu bintu Ka’abin; duk da cewa malamai sun yi sabani cikin kasancewar Mulaikatu cikin Matayen da Annabi ya taba aure, wasu sun tafi ya aure ta wasu kuma sun musanta batun.
Ta Bakwai, Akwai Fatimatu bintul Dahhaku, Annabi SAW ya aure ta sannan kuma ya rabu da ita, wani bayanin kuma ana cewa, Annabi SAW ya nemi aurenta a wurin Mahaifinta, sai ya ce Ya Rasulallahi, wance ba ta taba rashin lafiya ba, sai SAW ya ce ashe ba ta da ‘alheri’, rashin lafiya abu biyu ne, ko Allah ya kankare maka zunubi ko ya daga darajarka, sabida haka, Annabi SAW ya fasa aurenta.
Ta Takwas, Akwai Aliyatu bintu Zabyana bin Amr; Annabi SAW ya aure ta ya zauna da ita sannan ya rabu da ita. Ta Tara, akwai Kutailatu bintu Kaisin (‘yar’uwar Ash’as bin Kaisin) shi ne ya aura wa Annabi SAW ‘yar uwarsa a shekara ta Goma da Hijra, daga baya Dan’uwanta ya ce zai kai ta ganin gida Yamen, sun tafi ganin Gida kafin su dawo Annabi SAW ya rasu.
Ta Goma, Akwai Sana bintu Asma’a Sullami, ita ma ta rasu kafin Annabi SAW ya tare da ita, amma a Ruwayar ibni Is’haka, ya ce Annabi Sakarta ya yi. Ta 11, Akwa Sharahu bintu Hanifata (‘yar’uwar Duhyatul kalbi), ita ma ta rasu kafin Annabi SAW ya tare da ita. Akwai Laila bintul Kadi (‘yar’uwar Kaisin); ita kuma ta kasance Mace ce mai tsananin kishi, Gidan Annabi SAW kuwa, Gida ne cike da Mata, sabida haka ta ce, Ya Rasulallahi ya sallame ta, ba za ta iya zama da kishiyoyi ba. Ikon Allah kuwa, Kura ce ta cinye ta a daji.
Sai ta karshe, Mace ce daga dangin Gifara (‘yar dangin su Abi Zarril Gifari); ita kuma Allah ya jarrabe ta da cuta a jiki, akwai cutar ‘albaras’ nau’in cutar kuturta a tare da ita, sai Annabi SAW ya yi mata Addu’ar samun lafiya sai ya sallame ta. Duk Abin da Annabi SAW ya yi mata na kayan aurenta, bai amsa komai ba sabida rashin lafiya ce.
An ruwaito wasu Matan kuma daban wadanda Annabi SAW ya nema amma bai zauna tare da su ba. Daga cikinsu akwai wata Mata daga kabilar Murrata bin Aufin da Annabi SAW ya nema a wurin mahaifinta, shi kuma mahaifin bai son bawa Annabi ‘yarsa, sai ya yi karya da cewa, tana da ciwon kuturta, yayin da ya koma gida sai ya sami yarinyar shi cikin ciwon kuturta.
Akwai wata ana kiranta Saudatu, Annabi SAW ya neme ta amma ita kuma ba ta da lafiya, ciwon tabin hankali yakan tasar mata, sai ta ce ya Rasulallahi, ina tsoron kar ciwon ya tashi in yi kuka zuwa kanka ya Rasulallah, sai Manzon Allah SAW ya yi mata addu’a ya kyale ta.
Sai wata kuma, ana kiranta Safiyyatu bintu Basshamata (Balarabiya ce, ba Bayahudiya ba); ita kuma Annabi SAW a cikin kuyangu ya same ta, sai Annabi SAW ya ba ta zabi, in ta yarda ya aure ta, in kuma tana son komawa wajen Mijinta na farko ta koma, sai ta zabi Mijinta na farko, Annabi SAW ya maida ita.
Ta Hudunsu kuma, Malamai ba su fadi sunanta ba, Annabi SAW ya nemi aurenta, sai ta ce za ta je ta nemi amincewar mahaifinta, a wannan lokaci, daga wani gari zuwa wani gari, tafiya ce mai daukar kwanaki, makonni wasu ma har watanni, bayan ta isa wurin mahaifinta, ta nemi izininsa, ta dawo, sai Annabi SAW ya ce mata, ‘ya lulluba da wani mayafin kafin ta dawo’, Manzon Allah SAW ya yi mata Magana da tsarin Alkur’ani (hunna libasul lakum, wa’antum libasul lahunna: su mayafi ne a gare ku, kuma mayafi ne a wurin su).
Manzon Allah SAW ya nemi auren Ummu Hani (‘yar’uwar Sayyidina Ali) da kansa, sai ta fada wa Annabi SAW cewa, tana da yara da yawa, ba za ta iya biyan hakkin aurenta ba sabida yara.
Ummu Hani tare suka taso da Annabi SAW, mahaifiyarta, Fatimatu bintu Asadin Matar Abu Dalibi ce, ita ce mahaifiyar Annabi SAW a wurin riko, Sayyada Fatima ta samo sunanta ne a wurin mahaifiyar Sayyidina Ali da Ummu Hani. Sai Manzon Allah SAW ya yi mata uzuri sabida ‘ya’ya.
Annabi SAW ya tambayi Jabiru bin Abdullahi kan matar da ya aura, ya ce masa, Budurwa ka aura ko Bazawara, sai ya ce, Bazawara, Annabi SAW ya ce masa kana yaro za ka auri Bazawara? Sai Jabiru ya ce, ya Rasulallahi, mahaifina ya rasu ya bar min kannai mata, budurwa ba za ta iya zama da su ba, shi ya sa na auri Bazawara.