Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Pate, ya ce asarar da ake samu a duk shekara a Nijeriya sakamakon cutar zazzabin cizon sauro ya zarce dala biliyan 1.1.
Pate ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da shawarwarin kawar da zazzabin cizon sauro a Nijeriya wanda ya gudana a Abuja.
- Leicester City Ta Kori Kocinta Bayan Rashin Nasara A Hannun Chelsea
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Biyu
Wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya, Alaba Balogun, ya fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa Pate ya bayyana cutar zazzabin cizon sauro ba wai matsalar kiwon lafiya kadai ba, amma matsalar tattalin arziki ne da ya kamata a kawar da ita.
Pate ya ce wannan yunkuri mataki ne mai kwarin gwiwa na yanke hukunci tinkarar cutar da magance ta.
Ya ce, “Maleriya na ci gaba da yin illar da ba za a amince da ita ba a Nijeriya, inda kashi 27 cikin 100 na masu fama da cutar zazzabin cizon sauro a duniya da kuma kashi 31 cikin 100 na mace-macen zazzabin cizon sauro a duniya, kasarmu ce tafi kowace kasa daukar nauyin wannan cuta. A cikin 2022, yara sama da 180,000 na Nijeriya ‘yan kasa da shekaru biyar sun rasa rayukansu sakamakon zazzabin cizon sauro. Muke da kayan aikin da za mu iya magance cutar.
“Wannan ba matsalar lafiya ba ce kawai, matakin gaggawa ce ga ci gaban tattalin arziki. Zazzabin cizon sauro yana rage yawan aiki, yana kara kashe kudin kiwon lafiya daga aljihu da kuma habaka kalubalen talauci. Nijeriya na asarar kudaden shiga duk shekara daga zazzabin cizon sauro wanda ya zarce dala biliyan 1.1, babban abin tunatarwa kan muhimmancin tattalin arziki na kawar da cutar.”
A cewarsa, kawar da zazzabin cizon sauro wani muhimmin bangare ne na tsarin sake zuba jari na sashen lafiya na Nijeriya don kawo sauyi a fannin kiwon lafiya, daidai da sabon ajandar da gwamnatin yanzu ke da shi.
Ya kuma bayyana muhimmancin shugabannin gargajiya da na addini don samar da goyon baya daga tushe da kuma tasiri wajen sauya halayya.
Karamin ministan lafiya da walwalar jama’a, Dakta Iziak Salako, ya tabbatar da kungiyar masu ba da shawara a matsayin gungun kwararru da za su ba da shawarwari masu inganci don taimakawa kasar nan wajen rage matsalar zazzabin cizon sauro da ba za a amince da ita ba tare da samar da sahihin hanyoyin da za a bi a Nijeriya.
“Domin mu samu nasara, kamfanoni masu zaman kansu da abokan huldar kasa da kasa da ma’aikatan kiwon lafiya da kuma al’ummomin da muke yi wa hidima dole ne mu hada kai,” in ji Salako.