Bisa kididdigar da cibiyar binciken sana’ar samar da hidimomi, ta hukumar kididdigar kasar Sin, da kungiyar hadin gwiwa ta jigilar kaya da sayayya ta kasar Sin suka fitar a yau Asabar 30 ga wannan wata, an ce, alkaluman sayar da kayayyaki na kamfanonin kasar Sin ko PMI na watan Nuwanba, sun kai kashi 50.3 cikin dari, adadin da ya karu da kashi 0.2 cikin dari bisa na watan da ya gabata.
Babban jami’in kididdiga na cibiyar binciken sana’ar samar da hidimomi, a hukumar kididdiga ta kasar Sin Zhao Qinghe ya bayyana cewa, ta hanyar aiwatar da manufofi da matakai a jere a watan na Nuwanba, alkaluman PMI sun karu zuwa kashi 50.3 cikin dari, yayin da aka fadada harkoki a wannan fanni.
Kana an inganta aikin samar da kayayyaki, da bukatun hajoji a wannan wata, inda ma’aunin samar da kaya a watan ya kai kashi 52.4 cikin dari, wanda ya karu da kashi 0.4 cikin dari bisa na watan da ya gabata, kuma ma’aunin sabbin yarjejeniyoyin bukatun kaya a wannan wata ya kai kashi 50.8 cikin dari, wanda ya karu da kashi 0.8 cikin dari bisa na watan da ya gabata.
Game da sana’o’in kasar kuwa, ma’aunin samar da na’urorin amfanin yau da kullum, da motoci a wannan wata, da kuma ma’aunin sabbin yarjejeniyoyin bukatun nau’o’in kayayyakin dukkansu, sun karu da fiye da kashi 54 cikin dari. (Zainab Zhang)