Jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood wanda ya na daya daga cikin wadanda tauraruwarsu ta dade ta na haskawa a wannan masana’antar Ali Rabi’u Ali ya bayyana cewar ana yiwa masu yin wannan sana’a ta fim a matsayin malamai ko wasu masu gyaran tarbiyya a lokacin baya.
Ali Rabi’u wanda ya ce ya shafe fiye da shekara 25 da ya fara wannan harka a matsayin mai daukar hoto zuwa jarumi zuwa furodusa da kuma darakta, ya yi bayanai da dama a kan wannan masana’antar a wata hira da ya yi da jaruma Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna Gabon’s Room Talk Show inda ya tabbatar da cewar zimmar da yake da ita na koyar da wasu abubuwan da ya sani ne ya sa har ya fara shirya fina finai da kansa.
- Bai Kamata Mutum Ya Dogara Da Harkar Fim Kadai Ba -Hamza Talle Mai Fata
- Tun Kafin A Samu Masana’antar Kannywood Nake Harkar Fim – Lilisco
Tunda farko dai Ali ya yi bayani akan yadda yake daukar samuwar manhajar YouTube a cikin masana’antar Kannywood ba kamar yadda aka sani a baya ba, inda ya ce shekaru 10 da suka gabata ya taba wannan maganar inda ya tabbatar da cewar nan gaba za a koma dora fina-finai a yanar gizo da kuma kafafin talabijin na Satellite wanda kuma ya ce maganar da ya yi ga ta yanzu a zahiri domin kuwa komai ya koma yanar gizo ko kuma gidajen talabijin.
Sannan kuma ya ce zuwan soshiyal midiya yana da amfani amma kuma a wani bangaren ya matukar kasaara wannan harka ta fim, domin kuwa a yanzu yayin da ake cikin daukar sabon fim sai kaga wani ya zaro waya a aljihunsa ya na daukar bidiyon duk wani abu da ake yi a wajen lakeshin dinka na fim ya dora a shafinsa na Facebook ko Tik Tok.
Hakan da ya yi zai sa mutane su fara ganin fitowar da ka tsara a cikin shirinka tun kafin shirin ya shiga kasuwa,da haka ne zai sa masu kallo ba za su matsu fim dinka ya shiga kasuwa ba domin sun riga da sun ga wasu daga cikin abubuwan da fim din ya kunsa,ba kamar a lokacin baya da mutane za su kagu wajen jiran fim ya fito su kalla ba, saboda haka wannan hali da wasu daga cikin wadanda suke masana’antar suke yi ya matukar ragewa kasuwar fina-finai yawan ciniki.
Da yake amsa tambaya a kan minene matsayarsa dangane da wadanda ke yi wa jaruman fim kallon mutanen banza, Ali ya ce a tasa fahimtar babu wani mutum da zai lalace bayan shigowarshi wannan masana’anta ta Kannywood,domin kuwa duk idan kaga wani dan iska a Kannywood to dama can dan iska ne domin masana’antar Kannywood babu wanda ta taba mayarwa dan iska kowa da irin halinsa ya shigo cikinta inji shi.
Ya ci gaba da cewa a zamanin baya kafin yanzu mutane su na yi mana kallon wasu mutane da ke gyaran tarbiyya ta hanyar fina finansu ko kuma wasu malamai da ke isar da sako ta wata hanyar da ba wa’azi ba, saboda haka duk wanda kagani dan iska a masana’antar Kannywood dama can dan iska ne ba Kannywood ya koyi iskanci ba Ali ya tabbatar.
A kan yadda wasu daga cikin Kannywood ke kuka da abinda suke kira butulci da suke ganin wasu daga cikin wadanda suka yi renonsu a masana’antar domin ganin sun tsaya da kafafunsu kuma daga baya su juya masu baya, Ali ya ce ko kusa bai hadu da irin wannan ba domin kuwa dama bai taimaki wani a masana’antar Kannywood domin jiran wata rana ya rama mashi ba.
A duk lokacin da na taimaki wani a wannam harka ba na sa ran cewar wata rana zan nemi taimako a wajensa balle ya ki yi mani har raina ya baci in ji, ya ci gaba da cewa akwai da dama daga cikin wadanda tauraruwarsu ke haskawa a yanzu wanda ni na rene su tun kafin su san minene fim,a duk lokacin da na ji wani ya yabe su ko ya nuna sun burge shi har kuka nake yi domin kuwa nasan ta dalilina ne wannan mutumin ya kai wannan matsayi da ake ganinshi a yanzu.
Daga karshe Ali Rabi’u Ali ya bayyana cewar zuciyarsa ba ta mutu a jiran wani ya yi mashi ba,duk da cewar duk wani alheri da ake samu a wata sana’a ya sami kwatankwacin irin nashi a harkar fim amma ya na hadawa da kasuwanci a gefe kuma yanzu haka shi ma’aikacin gwamnati ne hakan ya sa yana da hanyoyin samun kudade da dama ba tareda ya jira wani ya yi mashi ba.