Daya daga cikin manyan jarumai da aka dade ana damawa dasu a masana’antar Kannywood Shuaibu Idris wanda akafi sani da Lilisco ya bayyana abubuwa da dama da suka danganci rayuwarshi ta masana’antar Kannywood wadda ya shafe fiye da shekara 30 a cikinta.
Lilisco wanda ya yi shura a masana’antar Kannywood daga jarumi mai rawa da soyayya kafin ya rikide zuwa jarumi mai fitowa matsayin Dan Sandan hukumar yan sanda ta Nijeriya inda kuma yakan taka muhimmiyar rawa a duk lokacin da ya fito a irin wannnan aiki na jami’in tsaro, Lilisco ya ce ba shi ne ya zabi wannan role din ba amma tunda masu shirya fina-finai sun ga ya dace da wannan matsayi babu abinda ya dace ya yi illa ya yi iya kokarin shi wajen burge masu kallo a duk lokacin da ya fito a cikin fim.
- Na Fi Jin Dadin Rubutu In Na Gaji Tibis – Maryam Faruk
- Neymar Zai Yi Jinyar Mako Biyu Bayan Ya Sake Samun Rauni
Lilisco a wata hira da ya yi da jaruma Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna Gabon’s Room Talk Show ya ce asalinsa ma’aikaci ne a hukumar tarihi da raya al’adun gargajiya ta jahar Kano (Kano State History And Cultural Bureau) wanda hakan ne ya bashi kwarin gwiwar cewa zai iya wannan sana’a ta fim domin kuwa babban abinda ya iya a wancan lokacin shi ne rawa, wadda akan yi kala kala kama daga da gargajiya da kuma ta zamani.
Ya ci gaba da cewar tun kafin a samu wannan masana’antar ta Kannywood da nike alfahari da ita a yanzu na fara wannan harka ta Fim domin kuwa an taba daukata domin yin aikin wani fim a garuruwan Bauchi da Jos a shekarar 1991 shekaru 3 kafin samun wata masana’antar harkar fim a nan Jihar Kano.
Bayan an fara anan gida Kano sai na nuna sha’awar nima ina son in shiga harkar kuma cikin iyawar Allah na shiga da kafar dama, domin kuwa a wancan lokacin akwai wani fim da na yi a shekarar 1997 wanda ya samu daukaka sosai ya burge mutane har ya sa da dama daga cikin manyan masu shirya fim a wancan lokacin suka nuna sha’awar saka waka da rawa a fina finansu in ji shi.
Ana nan har furodusan shirin Sangaya ya bukaci in koya wa jaruman da zai saka a cikin shirin rawa, wadanda suka hada da Ali Nuhu, Fati Muhammad da kuma marigayiya Hauwa Ali Dodo, da haka ne ya zamana duk wani fim da za a yi sai an nemi in koyar da jaruman fim din rawar waka, wanda ni kuma a lokacin sai naga cewar da in ci gaba da yin fina-finai nawa na kaina ai kara in tsaya a wannan sabon aiki da nasamu tunda dama dai ni mai koyar da rawa ne inji Lilisco.
Da yake amsa tambaya a kan dalilin da yasa yanzu harkar gidajen sinima suka daina yin tasiri, Lilisco ya ce daga cikin abinda ya tauye harkar sinima a yanzu akwai shigowar media da kuma wayoyin hannu da suka yawaita a hannun mutane inda ya ce a lokacin baya idan sabon fim ya fito zakaga mutane suna tururuwar shiga gidajen sinima domin kallon sabbin fina-finai amma yanzu mutum na gidansa zaune zai saka data kawai ya kalla a YouTube ko wata manhajar yanar gizo ba tare da ya tafi sinima ba.
Hakan yasa yanzu mutane suka daina zuba kudadensu a harkar gidajen sinima domin kuwa koda ka saka kudi ka bude gidan sinima ba lallai bane ka iya mayar da kudaden da ka kashe ba kamar a lokacin baya da babu wata hanyar samun kudi a masana’antar Kannywood kamar sinima ba.
Daga karshe Shuaibu Idris ya karyata wadanda ke cewa jarumai mata a masana’antar Kannywood basu son zaman aure, inda ya ce ko kusa wannan magana babu kamshin gaskiya a cikinta domin kuwa yanzu haka matarsa ‘yar masana’antar Kannywood ce gaba da baya amma kuma sun shafe shekaru fiye da 20 a tare ba tare da wata matsala ba.
Maganar da ake yi na cewa jarumai mata a masana’antar Kannywood basu son zaman aure ba gaskiya ba ne don yanzu haka ina zaune da matata wadda take yar masana’antar Kannywood gaba da baya lami lafiya tsawon shekaru fiye da 20 ba tare da wata matsala ba,mun haifi ‘ya’ya biyar tare da ita sannan kuma tana kyautata mani bakin gwargwado nima ina kyautata mata iya zarafi na saboda haka idan naji wasu na irin wadannan maganganu sai dai inyi kurum saboda a ganina sai aure 1000 na wadanda ba yan Kannywood ba ya mutu kafin auren jarumar Kannywood daya ya mutu.