Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya kaddamar da shirin ci gaban al’umma na jihar. Manufofin shirin sun hada da inganta gina al’umma da bunkasa samar da ayyuka na asali, bunkasa tattalin arziki, karfafa tallafa wa al’umma da inganta daidaiton jinsi da kare hakkin Dan’adam.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, gwamna ya ce babban kwamitin aiki da cikawa na shirin na da rassa guda 3, babban kwamitin na karkashin jagorancin gwamnan, sai kwamitin tsare-tsare hadin guiwa karkashin jagorancin mataimakin gwamnan da kuma kwmaitin matakin al’umma da zai kunshi manyan masu ruwa da tsaki a al’ummomin karkara.
- Dikko Radda Ya Bai Wa Gwarazan Hikayata Kyautar Kudi
- ‘Yansanda Sun Ceto Fasinjoji 14 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina
Ya ce babbar manufar shirin shi ne farfado da jihar zuwa matakin da ya kamata. Gwamnan ya bayyana cewa duk da cimma al’ada da albarkatu a jihar, al’ummomin da ke karkara na fuskantar matsaloli da dama ta fuskar sha’anin kiwon lafiya, karancin samun tsaftataccen ruwan sha, yayin da matasa ke ta fafutukar samun damarmaki don inganta rayuwarsu.
Ya ce gwamnatin jiha ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen fito da tsare-tsare da shawo kan matsalolin. Gwamnan ya bayyana cewa makasudin shirin ci gaban al’umma shi ne domin sanya al’umma cikin sha’anin ayyukan ci gaba.
Mataimakin gwamnan wanda ya yi magana ta bakin kwamishinan kudi ya ce shirin ci gaban al’ummar zai tafi tare da mambobin al’ummomi wajen gano ayyuka har ma da tabbatar da ingancin aikin.