A kwanakin baya, firaministar kasar Samoa, Fiame Naomi Mata’afa, ta zanta da wani dan jarida na rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, inda ta yaba da yadda kasar Sin ke kula da harkokin kasa da kasa.
Fiame ta ce, a lokacin da ake fuskantar matsaloli, kasar Sin ta gabatar da dabarun da suka dace, na taimakawa kasashen duniya su iya tinkarar kalubale da samar da damammaki. Jami’ar ta ce kasar Sin ba ta cewa “Me za mu yi muku”? Maimakon haka ta kan ce “Wannan matsala ce da za mu warware tare”. Kasar Sin tana samar da damammaki ga dukkan kasashen duniya.
Bugu da kari, Fiame ta yaba musamman da matakan gyare-gyare da gwamnatin kasar Sin ke dauka, inda a ko da yaushe kasar ke kokarin fahimtar halin da ake ciki, da kuma tsarawa, da daidaita ayyukan gwamnati yadda ya kamata, don kara yin aiki mai inganci da amfani wajen biyan bukatun ciki da waje. (Safiyah Ma)