• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Katafaren Aikin Karkatar Da Ruwa Na Sin Ya Karkata Kyubik Mita Biliyan 76.5 Zuwa Arewacin Kasar

by CGTN Hausa and Sulaiman
11 months ago
DCIM100MEDIADJI_0023.JPG

DCIM100MEDIADJI_0023.JPG

Yayin wani dandalin tattauna batutuwan da suka shafi tsarin lura da ruwa, da bunkasa ingancin aikin karkatar da ruwa na kasar Sin, wanda ya gudana a jiya Asabar, an bayyana wasu alkaluma da suka nuna cewa, karkashin katafaren aikin karkatar da ruwa na kasar Sin, an yi nasarar karkata ruwa har kyubik mita biliyan 76.5 zuwa arewacin kasar.

An ce karkashin wannan muhimmin aiki, an karkata ruwa daga yankunan kudancin kasar zuwa arewacin kasar, wadanda ke fuskantar yiwuwar fama da fari.

  • Yawan Masu Amfani Da Manhajar Samar Da Nau’o’in Bayanai Ta Fasahar AI A Kasar Sin Ya Kai Miliyan 230
  • Atiku Ya Karɓi Baƙuncin Peter Obi A Adamawa 

Bayanai sun shaida cewa, aikin ya amfani sama da mutane miliyan 185, ya kuma samar da ruwa ga manya da matsakaitan biranen kasar Sin har 45, dake kan hanyoyinsa guda biyu.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

A bana ne ake bikin cikar wannan muhimmin aiki na karkatar da ruwa daga kudu zuwa arewacin Sin shekaru 10 da kaddamarwa. An kuma tsara zai kasance mai hanyoyi 3, wato hanyar tsakiya, da ta gabashi da yammaci.

Da yake tsokaci game da aikin, shugaban kamfanin dake aiwatar da shi Wang Annan, ya shaidawa dandalin na jiya Asabar cewa, aikin kyautata hanyar ruwan ta tsakiyar kasar Sin na gudana yadda ya kamata, kana makamancinsa na hanyar gabashi da kwarya-kwaryar aikin na hanyar yammaci, su ma suka ci gaba yadda ya kamata.

A cikin watanni 10 na farkon shekarar bana, jarin da kasar Sin ta zuba a ayyukan tsumin ruwa ya kai kusa kudin kasar yuan tiriliyan 1.09, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 151.66, adadin da ya karu da kaso 11.7 bisa dari kan na shekarar da ta gabata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
Next Post
Gwamna Radda Ya Kaddamar Da Shirin Ci Gaban Al’umma

Gwamna Radda Ya Kaddamar Da Shirin Ci Gaban Al’umma

LABARAI MASU NASABA

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

November 7, 2025
An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.