Olori Atuwatse III, ita ce ta kafa gidauniyar Elevate Africa, ta samu wannan karramawar ne saboda gudummawar da take bayarwa ga al’umma ta fuskar amfanar da su a fannonin ilimi da jagoranci nagari da tallafawa jama’a musamman mabuƙata.
Wasu daga cikin ɓangarorin da ta yi fice wanda suka kai ga samun wannan karramawar sun haɗa da tallafawa al’umma ta hannun gidauniyar “Royal Iwere Foundation (RIF)”, Olori, ta samar da shirye-shirye masu tasiri ga jama’a kamar horar da malamai da shirin ƙarfafa gwuiwa a fannin ƙirƙire-ƙirƙire da fannoni da dama wajen mayar da hankali a fannin inganta ilimi da kiwon lafiya da inganta tattalin arziƙi ga matasa, musamman ‘ya’ya mata da sauran al’umma.
- Katafaren Aikin Karkatar Da Ruwa Na Sin Ya Karkata Kyubik Mita Biliyan 76.5 Zuwa Arewacin Kasar
- Bankin Zenith Ya Tallafa Wa Matasa Da Naira Miliyan 77 A Jihar Legas
Ta kasance mamba a babban kwamitin bayar da shawarwari kan inganta harkokin mata a Nijeriya (HLAC), don bai wa mata damar dogaro a kai. Olori, ta haɗa kai da gwamnati a fafutukar da take na magance matsalolin da suka shafi mata da kawar da fifiko wajen samar da damarmaki.
Olori Atuwatse III, tana matuƙar ƙoƙari wajen ganin ci gaban matasa ta yadda take taka muhimmiyar rawa don samar wa matasan kayan aiki da ba su horo kan fasahar sana’o’i ta yadda za su dogara da kansu, wannan yunƙuri ya taimaka wajen kawar da zaman kashe wando a ƙasarnan, tare da bai wa matasa damar yin nasara wajen cimma burikansu na rayuwa.
Olori, mace ce mai matuƙar tasiri a duniya, kasancewarta ɗaya daga cikin Matan Afirka 100 masu tasiri a shekarar 2023, ta kuma taɓa yin alƙalanci a shirin gasar lambar yabo ta Diana a 2024, bugu da ƙari tana taka muhimmiyar rawa a matsayin mai bayar da shawara don samar da ingantaccen canji a duniya.
Baya da cewa ta yi karatu a fannin shari’a daga Makarantar Tattalin Arziki ta London, Olori, ta kafa manyan wuraren harkokin kasuwanci da yin nasara a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da fannin dinke-dinke da sauransu, ta kuma kasance ɗaya daga cikin masu jagorantar masana’antu da dama, inda ta bayar da bayar da gagarumar gudummawa wajen ɓunƙasa su.
Olori Atuwatse III, ta yi gadon mulki da tasiri a wajen al’umma, kasancewarta Sarauniyar Warri, kuma uwa ce mai kishin ƙasa wadda ta himmatu wajen barin gadon ilimi da ƙarfafa wa al’umma da samar musu da ci gaba mai ɗorewa a masarautar Warri da duniya baki ɗaya.
Olori Atuwatse III, mata ce ga Sarkin Warri Ogiame Atuwatse III, wanda suke da ‘ya’ya uku, rashin nasara ba ya daƙile mutum wajene cinma burinsa, sai dai ta haska masa ba ya kan turbar da zai kai ga nasarar da inda ya kamata ya bi. saboda haka akwai buƙatar ya sauya alkibla tare da ƙara ƙaimi.