Afirka ta Kudu da Nijeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniya don karfafa hadin gwiwa a bangaren kasuwanci, tattalin arziki, da tsaro.
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya sanar da fara bai wa ‘yan Nijeriya, musamman ‘yan kasuwa, bizar shekaru biyar ba tare da amfani da fasfo ba.
- An Gudanar Da Taron Gabatar Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Ciniki Cikin ‘Yanci Ta Hainan
- Yadda Za A Samu Sabuwar Damar Neman Ci Gaba Tare Bisa Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”
Ramaphosa ya ce wannan mataki zai saukaka tafiye-tafiye tsakanin kasashen biyu, musamman ga ‘yan kasuwa da masu yawon bude ido.
Ya kuma yi alkawarin cire wasu ka’idoji da ke hana saka jari, tare da magance matsalolin da kamfanoni ke fuskanta.
A cewar shugaban, wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen kara yawan jari tsakanin kasashen biyu, wanda zai samar da sabbin ayyuka da inganta rayuwar al’umma.
Ya ce Nijeriya na daya daga cikin manyan abokan kasuwanci na Afirka ta Kudu, kuma wannan matakin zai kara karfafa dangantakar tattalin arziki da siyasa.
Bugu da kari, kasashen biyu sun cimma matsaya kan bukatar yin aiki tare don yakar manyan laifuka da matsalolin tsaro da ke barazana ga yankin.
Wannan hadin gwiwar zai taimaka wajen inganta tsaro da bunkasa kasuwanci da saka jari.
Kazalika, kasashen sun amince su yi musanyar bayanai don yaki da manyan laifuka, barazanar tashin hankali, da cin zarafin ‘yan kasashen biyu.
Wannan na daga cikin matakan inganta alakar kasashen da tabbatar da amfanin bayanan da suka dace.