Hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO) ta sanya Bikin Bazara na sabuwar shekarar al’ummar Sinawa cikin jerin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da dan adam ya gada.
A yanke wannan shawara ce yayin taron kwamitin gwamnatoci domin kare al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba, wanda ke gudana a Paraguay daga ranar 2 zuwa 7 ga wata. Kwamitin ya sanya Bikin Bazara cikin jerin ne bisa la’akari da tarin al’adu da bukukuwan gargajiya na musamman da suka shafi daukacin al’ummar Sinawa.
- Afirka Ta Kudu Za Ta Fara Bai Wa ‘Yan Nijeriya Bizar Shekaru 5
- Tinubu Ya Amince Da Biyan Kuɗin Kafa Cibiyar Yaɗa Labarai Ta UNESCO
A cewar UNESCO, Bikin Bazarar, wadda ita ke alamta shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, na kunshe da shirye-shirye daban-daban, ciki har da addu’ar samun wadata da haduwa da iyalai. Haka kuma, akwai wasu shirye-shirye da dattawa ke tsarawa da kuma bukukuwa daban-daban da al’ummomi ke shiryawa domin mutane su halarta.
Kwamitin na UNESCO ya kuma nanata cewa, bikin yana kuma kunshe da alamomin nuna jituwa dake tsakanin mutane da halittu tare da bayar da gudunmuwa ga ci gaba mai dorewa a bangarori kamar na wadatar abinci da ilimi da kuma taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kai game da muhimmancin kare muhalli.
Da wannan kari da UNESCO ta yi cikin jerin, yanzu akwai wasu siffofi ko bukukuwan gargajiya na Sin 44 da hukumar ta sanya cikin jerin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da dan adam ya gada. (Fa’iza Mustapha)