Uwargidan Gwamnan Zamfara Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana takaicin ta kan yadda ake samu Jami’an tsaro da laifin cin zarafin Mata watau Fyafe, a kan haka ta yi kira ga mahukunta da su sanya duk Jami’an tsaro da aka kama da cin zarafin Mata a kafafen yada Labarai kamar yadda suke gabatar da masu laifi ga “Yan gidan Talabijin da Rediyo da Jaridu dan ya zamo izina ga sauran Jami’an tsaro.
Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana haka ne ranar Laraba rana ta uku na yaki da cin zarafin Mata wanda aka yi wa fyade da marasa galihu da ake tauye mahakokin su a Gusau babban birnin jihar.
- Ali Nuhu Ya Zama Jakadan Kamfanin Tsaftace Haƙora A Arewacin Nijeriya
- Gwamnoni Sun Miƙa Ta’aziyya Ga Waɗanda Wani Abu Ya Fashe Da Su A Mota A Zamfara
A jawabin ta, Huriyya Dauda ta bayyana cewa a jawaban da aka gudanar a yanzu ya tabbatar da cewa, fitatun mutane ne kuma sananu ake kamawa da laifin cin zarafin Mata don haka muka kaddamar da kwamitoci a kananan hukumomi don yaki da masu aikata wannan mumunan laifi dan kawo karshen su “.
“Kuma yau ga Litatafi nan na turancin mun fasara su zuwa Hausa zamu raba don mutane su gane illar cin zarafin Mata da kuma hukuncin da meyi zai gamu da shi.
Hajiya Huriyya ta kara da cewa, ba fyade ba ne kadai cin zarafin Mata akwai rashin basu hakkin su na kulawa ga mazajan su na rashin abinci da karatun ‘ya’ya mata da sauran su.
Don haka doka za ta yi aiki a kan duk wanda aka kama a Zamfara wadannan munana lafiya in ji Huriyya Dauda.
Kuma muna godiya ga Kwamishin kananan Hukumomi da masarautu Hon. Ahmad Yandi ya bayyana cewa, Ma’aikatar Kananan Hukumomi za su yi hadin gwiwa da Sarakunan mu goma sha tara wajen yaki da masu wannan mumunan laifi, kuma zamu dauki nauyin kara litatafan don shigar da su ko’ina a fadin jihar ta Zamfara.