Majalisar wakilai ta soki yadda gwamnatocin jihohi ke gudanar da zaben kananan hukumomi, inda ta bayyana shi a matsayin cin fuska ga dimokuradiyya.
A cewarsu, wannan lamari ya gurgunta ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi, kuma dole ne a magance lamarin domin a kiyaye ka’idojin dimokuradiyya.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-wadai Da Rufe Fadar Sarkin Kano
- Gwamnoni Sun Miƙa Ta’aziyya Ga Waɗanda Wani Abu Ya Fashe Da Su A Mota A Zamfara
Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen ya bayyana hakan ne a jawabinsa na bude taron tattaunawa kan gyara zaben kananan hukumomi da tsarin mulki na kasa, wanda kwamitin majalisar kan duba kundin tsarin mulki ya shirya a ranar Litinin da ta gabata a Abuja.
Tajuddeen ya ce, “Lokacin da zabubbuka suka kasance mara tsari, inda jam’iyya mai mulki ta mamaye dukkan mukamai, ya bayyana a fili muna cewa wanna cin fuska ne ga ka’idojin dimokuradiyya,” in ji Tajuddeen. Ya kara da cewa irin wadannan zabukan ba wai kawai na kawo cikas ga dimokuradiyya ba ne, har ma suna haifar da matukar damuwa game da daidaito da ayyukan kananan hukumomin.
“Wannan yanayin ba abin kunya ba ne kawai, yana kawo babbar barazana ga dimokuradiyyarmu. Yana haifar da mummunn yanayi, inda abubuwan da ba a so suke kutsawa cikin kananan hukumomi, galibi ba su da karfin da ake bukata da hangen nesa don gudanar da mulki yadda ya kamata.
“Saboda haka, kananan hukumomi sun zama ‘yan amshin shatan gwamnatocin jihohi ko kuma ‘yan amshin shata a hannun ubangidan siyasa wadanda ke yin magudin zabe domin samun riban kashin kai,” in ji shi.
Tajuddeen ya bayyana rashin isassun kudade a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da kananan hukumomi ke fuskanta. “Yawancin gwamnatocin kananan hukumomi suna aiki da kasafin kudin da bai isa ya sauke nauyin da ke kansu ba,” in ji shi.
Ya kuma jaddada batun ‘yancin cin gashin kai, inda ya ce gwamnatocin jihohi ne ke sarrafa kananan hukumomi, wanda hakan ke haifar da tsoma baki wajen yanke shawara. A cewarsa, wannan rashin ‘yancin kai ne kuma yana dakushe romon dimokuradiyya a matakin kananan hukumomi.
Rashin isassun iya aiki daga fannin albarkatun Dan’adam da tsare-tsaren hukumomi ya kuma kawo cikas ga ingantaccen shugabanci a matakin kananan hukumomi. Yawancin ma’aikatan kananan hukumomi ba su da horo da kwarewa da ake bukata don gudanar da ingantaccen aiki, wanda hakan ke shafar samar da ayyuka da kuma sauke nauyin al’umma wajen gudanar da mulkin kananan hukumomi.
A halin da ake ciki, mataimakin shugban majalisar wakilai, Benjamin Okezie Kalu, wanda shi ne ya shugaban kwamitin majalisar kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, ya jaddada bukatar hada karfi da karfe a tsakanin masu ruwa da tsaki domin samun gyara mai ma’ana a harkokin kananan hukumomin Nijeriya.