• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamfanin Turkiyya Ya Fara Aikin inganta Noman Zamani A Zamfara 

by Leadership Hausa and Sulaiman
11 months ago
Noman zamani

Wani fitaccen kamfanin ƙasar Turkiyya mai suna Direkci zai fara aikin samar da na’urorin zamani a harkar noma tare da samar da lambunan zamani domin bunƙasa noma a Jihar Zamfara.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, Nurullah Mehmet, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na cibiyar Direkci, ya jagoranci tawagar da suka kai wa Gwamna Dauda Lawal ziyarar aiki a ofishinsa a gidan gwamnati da ke Gusau.

  • Babu Uziri A Yaki Da Cin Zarafin Mata – Mohamed M. Fall
  • Shettima Ya Yaba Wa BUK Kan Bai Wa Dalibai Guraben Karatu Cikin Adalci

Kamfanin na ƙasar Turkiyya na shirin kawo sauyi a harkar noma a Jihar Zamfara ta hanyar noman auduga, da raƙe, da waken soya mai tarin yawa.

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

Baya ga noman gargajiya, cibiyar za ta bullo da hanyoyin noma na zamani, gami da amfani da fasaha wajen samar da lambuna da kiwon kaji, waɗanda za su ƙara inganta fannoni da dama a jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da samar da abinci da samar da ayyukan yi ga al’ummar Jihar Zamfara.

“Kamar yadda na yi alƙawari a lokacin yaƙin neman zabe, idan aka zabe ni, gwamnatina za ta mai da hankali kan tsaro, noma da samar da abinci, ilimi, kiwon lafiya, tattalin arziki, da ƙarfafawa al’umma.

“An san al’ummarmu a jihar Zamfara da noma. Burin mu shi ne mu farfaɗo da wannan fanni. Muna da burin tabbatar da tsaron jihar domin mutane su koma gonakinsu.

“Abu mai muhimmanci shi ne, bayan tabbatar da tsaro a gonaki, mataki na gaba shi ne samar da na’urorin zamani ga manoman mu, kasancewar mun riga mun sami filaye da ma’aikata.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa muke maraba da haɗin gwiwar masu zuba jari irin su Direkci.

“Na yi tafiya zuwa Turkiyya a watan Yuli, inda na ziyarci ayyukan gonaki, kiwo, ayyukan kiwon kaji, da kuma masana’antar sarrafa na’urorin ayyukan noma ta Turk. Cibiyar Direkci ta zo Zamfara ne domin bullo da ci gaban fasaha a harkar noma.”

A farko, Nurullah Mehmet, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Direkci, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ta fara a cikin ƙanƙanin lokaci.

“Kamfanin mu Direkci yana gudanar da ayyuka da dama a jihohi daban-daban na Nijeriya.

“Shirin noma na Direkci a jihar Zamfara zai inganta darajar noma tare da jawo zuba jari, da bunƙasa tattalin arzikin cikin gida.

“Shigo da lambunan zamani zai habaka noma a duk shekara, wajen kare amfani gona daga fari da sauran abubuwa.

“Noman zamani da na kiwon kaji za su samar da guraben aikin yi a matakai daban-daban, daga ma’aikatan gona zuwa ƙwararru a harkar noma.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 
Manyan Labarai

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
Manyan Labarai

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo
Manyan Labarai

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Next Post
Gwamnatin Kaduna Ta Gargaɗi Jami’anta Kan Rubutu A Kafafen Sadarwa 

Gwamnatin Kaduna Ta Gargaɗi Jami'anta Kan Rubutu A Kafafen Sadarwa 

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.