Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai gurfana a kotu a karon farko kan zargin cin hanci da rashawa a ranar Talata.
Ana zarginsa da aikata laifuka uku, ciki har da cin hanci, zamba, da cin amana.
- ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP
- Jami’ar Kwara Ta Rage Wa Masu Bukata Ta Musamman Kudin Karatu
Netanyahu shi ne firaministan Isra’ila da ya fi dadewa a kan mulki, kuma shi ne na farko a tarihin kasar da zai gurfana a kotu yana kan mulki kan zargin aikata manyan laifuka.
Netanyahu, ya yi kokarin hana ci gaba da shari’ar, yana mai cewa yakin da Isra’ila ke yi da Gaza da matsalolin tsaro sun fi muhimmanci.
Amma kotu ta bayar da umarnin ci gaba da shari’ar, wadda ake sa ran za ta ja hankalinsa sosai a wannan lokaci mai muhimmanci ga kasar.
Shari’ar ta fara shekaru hudu da suka wuce, amma Netanyahu ya nace cewa bai aikata wani laifi ba, yana zargin cewa wannan duka makarkashiya ce ta siyasa da ‘yan adawa ke yi masa.
Masu gabatar da kara sun zarge shi da bai wa kafafen yada labarai cin hanci domin su rika wallafa labarai masu kyau game da shi da gwamnatinsa.
Har ila yau, ana zarginsa da karbar kyautuka masu tsada domin taimaka wa wani attajirin da ke shirya fina-finan Amurka wajen cimma burinsa.