Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci sabbin mambobin Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) da su gudanar da harkokin sadarwa yadda ya dace da kuma bayar da gudunmawa ga cigaban ƙasa.
Ministan wanda ya samu wakilcin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Dakta Sulaiman Haruna, ya bayyana hakan ne a wajen taron rantsar da sababbin jami’an yaɗa labarai da hulɗa da jama’a da aka gudanar a Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Tarayya, Abuja.
- Sanatocin Kudu Maso Gabas Sun Bukaci Duba Kudirin Dokar Gyaran Haraji
- Netanyahu Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Zargin Rashawa
A nasa jawabin, Ministan ya jaddada muhimmiyar rawar da hulɗa da jama’a ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa.
Ya buƙaci waɗanda aka rantsar da su yi amfani da basirar su da ilimin su wajen daƙile yaɗa labaran ƙarya, inganta haɗin kai, da kuma ɗaukaka martabar Nijeriya a duniya.
“Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya ta daɗe tana zama ginshiƙin nagarta, tana ba da horo, ba da shaida, da kuma tsarin ɗa’a a fagen hulɗa da jama’a.
“Ta hanyar ƙoƙarin ta, NIPR ta samar da ƙwararrun masana da ke ci gaba da taka rawa wajen gina ƙasa,” inji shi.
Ya yaba wa shugabannin NIPR bisa jajircewar su wajen ciyar da wannan aiki gaba tare da jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na samar da ingantacciyar hanyar sadarwa a matsayin ginshiƙin shugabanci na gari.
Ya ce: “A matsayi na na Mai Girma Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, na himmatu wajen tabbatar da cewa tsarin sadarwar mu na da inganci, da gaskiya, kuma sun dace da ingantattun ayyuka.
“Wannan rantsarwar ta yi daidai da babban burin mu na ƙarfafa iyawar jami’an watsa labarai a duk sassan gwamnati domin su yi hulɗa da jama’a da kuma daƙile yaɗa labaran ƙarya yadda ya kamata.”
Ministan ya buƙaci waɗanda aka rantsar ɗin da su kiyaye ƙwarewa da riƙon amana, musamman a zamanin gidan yana, inda ya bayyana rawar da suke takawa a matsayin mai muhimmanci ga haɗin kan ƙasa da kuma bunƙasa al’adun gargajiyar Nijeriya.
“Ga sababbin membobin da aka rantsar, yau ne farkon wani sabon babi a tafiyar ku ta aiki.
“Aikin ku ba wai kawai yana nuna yadda ƙungiyarku ko cibiyar ku yake ba; yana nuni ga ɗaukacin al’ummar ƙasar. Ku kiyaye ƙa’idojin NIPR kuma ku kasance jakadun gaskiya da nagarta,” inji shi.
Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku, ya bayyana jin daɗin sa da shigar da sabbin mambobi cikin cibiyar.
Shugaban ya jaddada muhimmancin aikin hulɗa da jama’a, inda ya ce, “Ba sa’a kawai kuka yi ba, haƙiƙa kun samu albarka, domin a yanzu kun shiga cikin aikin fitattun mutane, aiki ɗaya tilo da ba ya tsufa, aiki ɗaya tilo da ke mu ku jagorar samun abubuwa mafi kyawu daga rayuwa.”
Shugaban ya miƙa godiyar sa ga Ministan Yaɗa Labarai bisa rawar da ya taka wajen inganta harkar hulɗa da jama’a.
Ya bayyana ƙoƙarin da Ministan ya yi wajen ganin an amince da hulɗa da jama’a a matsayin aiki a aikin gwamnati.
“A shekarar da ta gabata, ya ɗauki nauyin rubutawa majalisa ta 45 kan kafawar a Bauchi, kuma a ranar 13 ga Disamba, 2023, majalisar ta yi la’akari da wannan takardar kuma ta amince da shi,” inji shugaban.
“Wannan wani muhimmin cigaba ne ga aikin mu, saboda yana nuna mahimmancin sadarwa mai inganci a cikin shugabanci.”
Ya nanata muhimmancin jami’an hulɗa da jama’a wajen samar da amana da fahimtar juna tsakanin gwamnati da jama’a.
“Idan aka yi hulɗa da jama’a yadda ya kamata, za su mallaki shirye-shiryen gwamnati. Idan aka yi hulɗa da jama’a yadda ya kamata, suna ba da shawarar abin da ya kamata a yi. Idan aka bai wa ‘yan kasa damar bayyana ra’ayoyinsu, yana da matuƙar amfani wajen samar da daidaito,” inji shi.