Yayin da kasar Sin ke ta aiwatar da matakai daban daban na zamanantar da kai, tare da gayyatar sassan kasa da kasa su shiga a dama da su cikin manufofin cimma nasara tare, masharhanta na kara jinjinawa alkiblar kasar ta rungumar dukkanin sassa don a gudu tare a tsira tare, a wani yanayi da ya saba da abun da aka saba gani daga akasarin kasashe yamma masu karfin fada a ji.
A ganina kasashen yamma da dama da suka yi mulkin mallaka a kasashe masu tasowa, sun gaza taimakawa irin wadannan kasashe wajen samun ci gaban da ya dace, maimakon hakan, wasu daga cikinsu sun fi son tabbatar da tasiri, da danniya, da kwashe albarkatun kasashen da suka mulka domin gajiyar kansu, amma sabanin haka, kasar Sin ta zo da sabon salo na zamanantarwa mai bude kofa, da burin tafiya tare da kowa, ta yadda za a kai ga samar da al’ummar bil adama ta zamani mai makomar bai daya.
- Birnin Yiwu Na Kasar Sin Zai Kaddamar Da Sabon Zagaye Na Gyare-gyaren Cinikayyar Duniya
- Beijing Za Ta Gudanar Da Dandalin Tattaunawa Kan Hanyoyin Da Za A Bi Wajen Tafiyar Da Harkokin Birane
Shaidu na zahiri sun nuna yadda kasar Sin ke shiga a dama da ita wajen ingiza ci gaban sassan kasashen duniya daban daban, inda take tabbatar da gajiyar ci gaban duniya bai takaita ga wasu sassa ’yan kalilan ba.
Shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, daya ce daga manyan misalai na manufofin da kasar Sin ta gabatarwa duniya domin bunkasa zamanintar da dukkanin kasashen duniya, inda a karkashin shawarar, Sin din take ta aiwatar da hadin gwiwa da sauran sassan kasashen duniya musamman masu tasowa, wajen samar da ababen more rayuwa, da zuba jarin raya kasashe. Sin na daukar wannan shawara a matsayin gudummawarta ta raba ribar ci gaba, da ingiza ci gaban tattalin arziki, da zamanintar da sassa daban daban abokan tafiya.
Ko shakka babu salon zamanantarwa na Sin, wanda ya tanadi raba kwarewa da alherai daban daban tare da sauran sassa, ta yadda su ma za su samu ci gaba, ya zamo wata haja mai daraja, wadda tarihin bil adama ba zai taba mantawa da ita ba!