• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kungiyoyin Sa-ido Na Kasa-da-kasa Sun Yaba Da Zaben Ghana

by Rabi'u Ali Indabawa
10 months ago
Ghana

Ƙungiyoyin sun yaba wa Ghana da ‘yan kasar bisa gudanar da zaben Shugaban kasa da na Majalisun dokoki cikin lumana.

Kungiyoyin da suka fito daga Tarayyar Afirka (AU), Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), da kungiyar Commonwealth a wani taron manema labarai na hadin gwiwa, sun yaba wa hukumar zabe (EC), jami’an zabe, jam’iyyun siyasa, ‘yansanda, da kafofin yada labarai kan rawar da suka taka wajen tabbatar da nasarar gudanar da zaben a Ghana.

  • ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP
  • Motoci Kirar Kamfanin Kasar Sin Na Samun Karin Karbuwa A Kasar Ghana

Da take jawabi a taron manema labaran a Accra babban birnin Ghana, Sahle-Work Zewde, tsohuwar Shugabar kasar Habasha kuma Shugabar tawagar sa ido kan zabe a Tarayyar Afirka (AUEOM) ta ce, an gudanar da zaben cikin lumana da kara tabbatar da dimokuradiyyar kasar. Ta ce, ‘Tawagar masu sa ido a zabukan kasashen tarayyar Afirka (AUEOM) ta yaba wa al’ummar Ghana bisa jajircewar da suka yi na tabbatar da tsarin dimokuradiyya, wanda hakan ke nuni da yadda aka gudanar da babban zaben kasar a ranar 7 ga watan Disamban 2024 cikin lumana. Gaba daya tsarin zaben ya bi ka’idodin yankin kasa da kasa, da kara karfafa kimar dimokradiyyar Ghana.

Alhaji Mohammed Namadi Sambo, tsohon mataimakin Shugaban Nijeriya kuma jagoran tawagar sa ido a kungiyar ECOWAS, ya ce masu kada kuri’a sun yi zabe cikin yanayi mai kyau, ba tare da tsangwama ko takurawa ba. Ta kuma taya al’ummar kasar Ghana murna. ‘Tawagar masu sa ido kan zabe ta Ecowas na taya al’ummar Ghana murna, tare da yi musu fatan ci gaba da samun zaman lafiya, daukaka, da ci gaba.”

Kungiyar sa ido ta ECOWAS ta jinjinawa Shugaban Ghana mai barin gado, Nana Akufo-Addo bisa yadda ya jagoranci kasar na shekaru 8, daya daga cikin mambar kungiyar.

LABARAI MASU NASABA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Kungiyar sa ido ta Commonwealth a karkashin jagorancin tsohon Shugaban kasar Botswana, Dokta Mokgweetsi Masisi ta ce, sun lura an bai wa nakasassu da tsoffi fifiko kuma an ba wa masu fama da matsalar gani da ido hakkinsu a wasu rumfunan zabe. Sai dai kuma sun lura da kalubale a wasu rumfunan zabe don wurin kada kuri’a ya yi wa masu amfani da keken guragu nisa.

Ya kara da cewa, ‘Rahoton su na karshe mai dauke da muhimman shawarwari za su mika shi ga babban sakatare kuma a raba shi zuwa ga gwamnatin Jamhuriyyar Ghana da sauran masu ruwa da tsaki da sauran jama’a.

A gefen taron, tsohon mataimakin Shugaban Nijeriya, kuma jagoran tawagar kungiyar ECOWAS ya yaba wa hukumomi da al’ummar Ghana bisa yadda aka gudanar da zaben kan tsari, a hira ta musamman da Muryar Amurka.

Tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama, na babbar jam’iyar adawa ta NDC, wanda ya lashe zaben Ghanan da kashi 56.55 cikin 100 na kuri’un da aka kada, ya yi jawabin amincewa da nasararsa bayan da hukumar zabe ta ayyana shi, a matsayin wanda ya lashe zaben kasar a hukumance.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga
Kasashen Ketare

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Next Post
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Muhimmiyar Makalar Xi Mai Taken “Zurfafa Aiwatar Da Juyin Juya Halin Jam’iyyar Kwaminis Ta Sin”

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Muhimmiyar Makalar Xi Mai Taken “Zurfafa Aiwatar Da Juyin Juya Halin Jam'iyyar Kwaminis Ta Sin”

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.