Hukumar Kula da Lantarki ta N8jeriya (NERC), ta bayyana cewa tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa wajen samar da lantarki ya karu zuwa Naira biliyan 199.64 a watan Disamba 2024.
Rahoton ya nuna cewa tallafin ya karu da kashi 2.76 cikin 100, daga Naira biliyan 194.26 a watan Nuwamba 2024.
- Manufar Sin Ta Yada Zango Ba Tare Da Biza Ba Ta Kara Jawo Hankalin Masu Yawon Shakatawa Na Ketare
- Da Dumi-Dumi: An Yi Kutse A Shafin Hukumar Kididdiga Ta Kasa
Karin ya faru ne sakamakon sauye-sauyen kudin musaya, inda dala ta kai Naira 1,687.45, da kuma karuwar hauhawar farashi da ta kai kashi 33.9 cikin 100.
NERC ta kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bar farashin wutar lantarki yadda yake ga dukkan rukunonin masu amfani.
Kwastomomin da ke kan matakin “A” suna biyan Naira 209 kan kowanne kilowat, yayin da farashin na matakin “E” ya ci gaba da zama yadda yake tun Disamban 2022.
Wannan karin tallafin ya nuna yadda gwamnati ke kokarin magance matsalar wutar lantarki a kasar.