Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur zuwa Naira 899.50 kan kowace lita, daga Naira 970.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, kamfanin ya ce wannan mataki yana da nufin rage wa ‘yan Nijeriya tsadar kudin sufuri yayin bukukuwan karshen shekara.
- Hatsarin Kwale-Kwale Ya Hallaka Mutane 13 A Indiya
- Ibadan: Ƙananan Yara da Yawa Sun Mutu A Turmutsitsi A Wajen Bikin Al’adu
Har ila yau, kamfanin ya kaddamar da wani sabon tsari, inda mutane za su iya siyan karin lita daya a kan bashi idan har suna amfani bankin Access Bank, First Bank, ko Zenith Bank.
Kamfanin ya gode wa ‘yan Nijeriya bisa goyon bayansu, tare da jaddada aniyar samar da man fetur mai inganci da arha.
Matatar Dangote, mai karfin tace gangar mai 650,000 a kowace rana, ita ce daya daga cikin mafi girma a duniya.
Kuma matatar za ta iya samar da dukkanin man fetur din da Nijeriya ke bukata da kuma wanda za ake fita da shi zuwa kasashen waje, matukar komai ya kankama.