Hukumar kula da sufurin jiragen saman fasinjoji ta kasar Sin (CAAC) ta ce kamfanonin jiragen sama na kasar sun yi tafiye-tafiye miliyan 700 a bana, wanda ya zama adadi mafi yawa a tarihin sufurin jiragen sama na kasar Sin.
Bisa alkaluman hukumar CAAC, daga farkon bana zuwa ranar Lahadin da ta gabata, kamfanonin jiragen sama na kasar sun yi tafiye-tafiye miliyan 700.48 dauke da fasinjoji, idan aka kwatanta da na shekarar 2023 da aka yi tafiye-tafiye miliyan 620.
- Da Dumi-Dumi: Dangote Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa N899 Kan Kowace Lita
- Da Dumi-Dumi: An Yi Kutse A Shafin Hukumar Kididdiga Ta Kasa
A cewar hukumar, tafiye-tafiye a cikin gida ne suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen ingiza farfadowar kasuwar sufurin jiragen saman fasinjoji a shekarar 2024, inda aka yi tafiye-tafiye miliyan 640, karuwar kaso 14 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2019 kafin bullar cutar COVID-19.
Haka zalika an samu ci gaba a bangaren zirga-zirga zuwa kasashen ketare, inda aka yi tafiye-tafiye miliyan 60 a bana. Wannan bangare ya samu karuwar kaso 130 a duniya, biyo bayan sassauta matakan takaita tafiye-tafiye da karuwar bukatu. (Fa’iza Mustapha)