Yankin musamman na Macao na kasar Sin na gab da kara shiga wani babi na ci gaba. Yayin da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ke bikin cika shekaru 25 da dawowar yankin karkashin ikon kasar, kafar yada labarai ta kasar Sin CGTN da cibiyar nazarin harkokin Macao, sun gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a kan mutane 1,551 na Macao, wanda ya nuna nasarar da aka samu wajen aiwatar da manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu” a Macao.
A bangaren nazarin gamsuwar jama’a game da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a Macao, kaso 93.9 na wadanda suka bayar da amsa, sun amince da ayyukan gwamnatin yankin a shekarun baya-bayan nan. Farin ciki da gamsuwar da mazauna yankin Macao suka nuna, alama ce ta gagarumar nasarar da Macao ya samu ta fuskar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa cikin shekaru 25 da suka gabata.
- Tallafin Wutar Lantarki Ya Kai Naira Biliyan 199.64 A Nijeriya – NERC
- Tattalin Arzikin Kasar Sin A Matsayin Bango Majinginar Duniya
Alkaluma sun nuna cewa, ma’aunin tattalin arziki na GDP na Macao, ya karu da sau 7.3 daga shekarar 1999 zuwa ta 2023. Kana a shekarar 2023, darajar cinikayya tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Macao, ya kai dalar Amurka biliyan 3.84, wanda ya karu da sau 4.3 idan aka kwatanta da kafin dawowarsa karkashin babban yankin Sin.
Ci gaba da kwanciyar hankalin Macao ya dogara ne da manufar “Kasa Daya” kuma tabbatuwar hakan ta dogara ne da hadawa da aiwatar da “Tsarin Mulki Biyu” mai kuzari na musammam.
Har ila yau, kaso 93.9 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana kwarin gwiwa kan aiwatar da manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu” da kuma manufar “Al’ummar Macao su Jagoranci Macao”. (Fa’iza Mustapha)