Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kashe naira biliyan 15 domin gyaran makarantu da samar da motoci a hukumance ga alkalan manyan kotuna da Khadis na kotunan Shari’ar Musulunci.
Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman majalisar zartarwa ta jihar a ranar Alhamis, kwamishinan ilimi, Alhaji Tukur Arkali, ya ce an amince da Naira miliyan 788.2 da Naira miliyan 591.4 da kuma Naira miliyan 433.1 don gyara Kwalejin ‘Sheikh Gummi Memorial College’; makarantar sakandire ta larabci ta Hafsatu Ahmadu Bello da kuma Kwalejin fasaha ta sokoto.
- Sojoji Sun Tarwatsa Sansanin Lakurawa A Sokoto Da Kebbi, Tare Da Ƙwato Makamai
- Shugaban Sin Ya Jinjinawa Nasarorin Da Yankin Macao Ya Samu Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata
Sauran makarantun da za a gyara sun hada da makarantar sakandire ta Unity, Bodinga a kan Naira miliyan 567,5; makarantar sakandiren Sani Dingyadi Unity, Farfaru akan Naira miliyan 374.6 da kuma cibiyar darusan karatuttukan Alkur’ani da sauran fannoni ta Sultan Maccido akan Naira biliyan 1.6
Bugu da kari, an sake amincewa da Naira biliyan 1.3 da Naira miliyan 591.4 domin gyara makarantar sakandiren mata ta gwamnati, Illela da sakandiren gwamnati illela da ambaliyar ruwa ta lalata.
Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Alhaji Bala Kokani ya kara bayyana cewa, an amince da kudi Naira miliyan 710.6 da kuma Naira miliyan 105.8 domin gyara gine-ginen da suka ruguje a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Sakkwato da Kwalejin Ahmadu Bello da ke Farfaru.
Hakazalika, an amince da kashe Naira miliyan 250 da Naira miliyan 122 domin gyara gidajen ma’aikatan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Umaru Ali Shinkafi Sokoto, da gina katafaren bandakai guda tara a harabar makarantar.
Bugu da kari, majalisar ta amince da siyan motocin jeeps guda 22 (na 2024) kan kudi Naira biliyan 2.4 ga alkalan manyan kotuna da kadis na kotun Shari’ar Musulunci.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Alhaji Sambo Bello Danchadi, ya ce majalisar ta kuma amince da kwangilar samar da sabuwar na’urar watsa labarai ta Rima FM Sokoto da kuma gyaran antenar gidan rediyon AM da ke kan antena mai nauyin 50 (kilowatts) akan kudi Naira miliyan 926.
Ya kuma bayyana amincewar majalisar kan gyaran injin janareta mai karfin wuta kilowatt 2000 na hukumar kula da samar da ruwa ta jihar sokoto akan kudi naira miliyan 80,850.