Jarin kai tsaye na Sin a kasashen waje wanda ba na tsabar kudi ba, ya karu da kaso 11.2 zuwa dalar Amurka biliyan 128.63 a watanni 11 na farkon bana.
Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar ta ce, daga watan Janairu zuwa Nuwamba, jarin kai tsaye da ba na tsabar kudi ba da kamfanonin Sin suka zuba a kasashen dake aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, ya karu kan na bara da kaso 5.1, zuwa dala biliyan 30.17.
- Yadda Ciniki Ya Habaka Tsakanin Babban Yankin Kasar Sin Da Yankin Macao A Fiye Da Shekaru 25
- Yankin Macao Ya Nuna Kuzarin Manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu”
Haka kuma a wannan lokaci, jimilar kudin ayyukan da kamfanonin Sin suka aiwatar a kasashen waje ta kai dala biliyan 140.23, karuwar kaso 3.4, kuma darajar sabbin ayyuka ta karu da kaso 11.9 zuwa dala biliyan 198.79.
Haka zalika, kudin ayyukan kwangila da kamfanonin Sin suka yi a kasashen dake aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ya kai dala biliyan 116.14 a wannan lokaci, karuwar kaso 2.5 kan na bara. Yayin da darajar sabbin kwangiloli da kamfanonin Sin suka rattabawa hannu a wadannan kasashe ya kai dala biliyan 167.95, karuwar kaso 11.8. (Fa’iza Mustapha)