Kasar Sin ta ce, tana fatan Tarayyar Turai EU za ta dauki kwararan matakai nan ba da jimawa ba, domin su hada hannu wajen samun ci gaba kan tattaunawarsu game da yarjejeniyar tsayar da farashin motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin.
Kakakin ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin He Yongqian ce ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai, bayan an mata tambaya game da inda aka tsaya kan tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu.
Ta kara da cewa, har kullum, kasar Sin ta kasance mai son warware takkadamar cinikayya ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna, kuma tana iya bakin kokarin yin hakan game da batun farashin. (Fa’iza Mustapha)