Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wolverhampton Wanderers da ke buga gasar Firimiya Lig ta naɗa tsohon Kocin FC Porto Vitor Pereira a matsayin sabon Kocinta, gogaggen Kocin ɗan ƙasar Portugal ya koma ƙungiyar Al-Shabab ta Saudi Pro League kan kwantiragin watanni 18, inda Wolves ta biya kusan fam 825,000 a matsayin kuɗin fansa.
Ya maye gurbin Gary O’Neil, wanda aka kora ranar Lahadi sakamakon rashin nasara da suka yi a gidan Ipswich da ci 2-1 ranar Asabar, wanda ya bar Wolves matsayi na biyu a matakin ƙarshe na gasar Premier.
- Liverpool Ta Samu Tazarar Maki 8 Akan Teburin Gasar Firimiyar Ingila
- Yau Ake Kece Raini Tsakanin Kungiyoyin Hamayya Na Manchester A Firimiyar Ingila
Pereira ya bayar da horo a karon farko a ranar Alhamis kuma wasansa na farko shi ne wasan da za ta yi da Leicester ranar Lahadi, wadda ke mataki na 17 a kan teburi da maki biyar tsakaninta da Wolves.
Wolves dai sun shafe makwanni da dama suna tantance zaɓinsu,kuma sun fitar da sunayen ‘yan takara ciki har da tsohon kocin West Ham David Moyes, Pereira wanda ya lashe manyan kofuna tare da Porto a shekarun 2012 da 2013 da kuma Super League na Girka tare da Olympiakos a 2015 ne ya samu nasarar zuwa Molineux Stadium a matsayin Koci.
Tun a watan Fabrairu ne yake jagorantar ƙungiyar ta Al-Shabab kuma ya bar su a matsayi na shida a gasar Saudi Pro League,Pereira mai shekaru 56 ya gaji O’Neil, wanda aka naɗa a Molineux a watan Agustan 2023, Wolves ta yi rashin nasara a wasanni 11 cikin 16 na gasar Premier bana.