Wani turmutsutsi da ya afku lokacin rabon shinkafa a Cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Maitama, Abuja, ya yi sanadin mutuwar mutum 10 a safiyar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa galibin wadanda suka rasa rayukansu mata da kananan yara ne, wadanda suka halarci cocin domin karɓar kayan agaji da suka haɗa da shinkafa, a wani bangare na ayyukan tallafi na shekara-shekara da cocin ke yi.
- ASUU Ta Yi Kira Ga Majalisar Kasa Ta Cire TETfund Daga Tsarin Sabuwar Dokar Haraji
- Kudin Kirifto: An Cafke Dan Nijeriya Da Laifin Damfarar ‘Yan Australiya Dala Miliyan 8
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 6:30 na safe.
Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce turmutsutsin ya yi sanadin mutuwar mutane 10, ciki har da yara huÉ—u.
Haka kuma, mutane takwas sun jikkata, inda huÉ—u daga cikinsu aka sallame su daga asibiti bayan samun kulawa, yayin da sauran ke ci gaba da jinya.