Hukumar leken asirin Burtaniya ta dakile yunkurin kashe Fafaroma Francis a wani lokacin da ya kai wata ziyara Iraki.
Wannan labarin na cikin tsakuren littafin tarihin rayuwarsa da ake dako, inda a ciki ya rubuta cewa bayan ya isa birnin Baghdad a watan Maris na 2021 ne aka sanar da shi cewa taron da zai halarta, akwai masu harin kunar bakin wake guda biyu da suke tarwatsa mutane.
- Morocco Za Ta Sake Karbar Bakuncin WAFCON A 2026
- Kudirin Dokar Haramta Amfani Da Kudaden Waje Ya Tsallake Karatu Na Farko A Majalisa
Daga bisani an kama mutanen da suke shirin kai harin.
Ziyarar ce ta farko da wani fafaroma zai kai a kasar Iraki, wadda kuma ya yi a lokacin da ake tsaka da annobar Korona.
“Kusan duk wadanda na yi shawara da su, sai da suka nuna min rashin amincewarsu da ziyarar,” in ji shi, sannan ya kara da cewa shi kuma ya yi tunanin ziyara ce mai matukar muhimmanci.
Jawabin Janar Tiani Ranar Cika Shekaru 66 Da Nijar Ta Zama Jamhuriya
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuryar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi jawabi ga al’umma ranar bikin samun ‘yancin kai inda ya tabo mahimman batutuwan da suka shafi tafiyar kasar daga lokacin da ya kwaci madafun iko zuwa yau.
A jawabin na mintocin kusan 30, shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar ya yi bitar nasarorin da aka samu daga darewar CNSP kan karaga kawo yau.
Ya ce ” Mun kori sojojin kasashen waje ba tare da nuna kyama ko wata rigima ba wadanda a baya suke yi wa ‘yancin kasarmu barazana suna kuma hana dakarunmu sukunin gudanar da aikinsu kamar yadda ya dace. Haka kuma, mun soke dukkan wasu kwangiloli da dukkan wasu dokoki da yarjeniyoyi na rashin adalci wadanda ba sa amfana wa Nijer komai, kuma su ke dakushe ci gabanta.
Sannan ya ce an yi nasara wajen hada kan al’umma a game da abin da ya shafi muradun kasa ma’ana, daga yanzu dukkan ‘yan Nijer alkibla daya suke kallo. A yau Nijer ta gwada cewa, za ta iya tsayuwa da kafafunta ta tunkari matsalolin ta’addanci ta kuma yi nasara, ta biya albashin ma’aikatanta ta kuma dauki dawainiyar bukatun kanta da kanta.
Janar Tiani ya ce, kasar za ta iya rayuwa ba tare da jiran tallafin da ake cewa tana samu daga waje ba wadanda wani bi ake fakewa da su don yi wa ‘yan Nijer barazana ko a wulakanta su.
Ya kuma bayyana cewa, “A karon farko a tarihin Nijer, dukkan wasu matakai da suka shafi kasar da ‘ya’yanta ana daukansu ne a nan gida daga ‘yan kasa domin amfanin Nijer, dalilin haka ne ma ya sa duk da mawuyacin halin da ake ciki aka dauki matakin samar da sassaucin rayuwa ga al’umma ta hanyar rage kudin man fetur da rage kudin likita da rage farashin siminti.”
Ya na mai alfahari da sabuwar alakar kasar da wasu kasashen waje.
A game da batun ficewa daga CEDEAO ya nanata cewa, ba makawa, kasashen nan 3 sun balle ba fashi domin kare ‘yancin kai da tabbatar da tsaro a yankin. Ya ce wanan kuma mataki ne da ke toshe dukkan hanyoyin da manyan kasashe ke bi su fake da CEDEAO su yaki kasashen AES.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan, ya sake nanata alkawalin rike amanar da ya dauka, ya jinjina wa dakarun tsaro saboda jajircewarsu akan tsaron kasa a wannan lokaci na gwabza yaki da ‘yan ta’adda, haka kuma ya yaba wa al’ummar kasar sabili da yadda suke ci gaba da nuna juriya kan mawuyacin halin da ake ciki.