Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA) ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe mutane 14 a wani hari da suka kai da tsakar dare ranar Lahadi a Æ™auyen Ri Do, wanda ke Æ™aramar hukumar Riyom ta jihar Filato, inda mafi yawan mazauna Æ™abilar Irigwe ne ke zaune.
A wata sanarwa da ƙungiyar IDA ta fitar ta hannun Sakataren yaɗa labaranta, Sam Jugo, ta bayyana cewa bayan samun labarin harin, ƙungiyar ta aika da wani wakilinta don tabbatar da gaskiyar lamarin.
Ya ce sun tabbatar da cewa an kashe mutane 14, yayin da wata mata mai suna Linda Moses mai shekaru 32 ta ji munanan raunuka, kuma a take aka fara ba ta kulawa.
Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomi da su ƙara tsaurara matakan tsaro don hana sake aukuwar irin wannan hari ko ramuwar gayya.
Har ila yau, sun bayyana cewa suna fatan hukumomi za su ɗauki matakin da ya dace yayin da al’ummar ke shirin birne gawarwakin waɗanda suka rasa rayukansu.
A nata É“angaren, gwamnatin Jihar Filato ta bakin Kwamishinan yaÉ—a labarai da sadarwa, Musa Ashoms, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Gwamnatin ta yi Allah-wadai da harin, inda ta yi kira ga jami’an tsaro su gudanar da bincike don gano waɗanda suka kai harin tare da tabbatar da cewa an hukunta su.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, da kakakin rundunar dakarun haɗin gwuiwa (OPSH), Manjo Samson Zhakom, ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin ba.