Gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin ci gaba da kokari wajen bayar da kariya ga muhallin halittun Rawayen Kogi, wanda yake kogi na biyu mafi tsawo a kasar, da aka fi sani da “uwar kogunan kasar”.
Mataimakin firaministan kasar Sin, Liu Guozhong ya bayyana a yayin wani taron zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin cewa, majalisar gudanarwar kasar da hukumomin da abin ya shafa, za su yi amfani da wani tsari mai tsauri domin kare albarkatun ruwa da ke kogin da kuma amfani da su yadda ya kamata.
A yayin taron dai, ‘yan majalisar wakilan jama’ar kasar sun tattauna a kan rahoton da aka bayar game da aikin kare Rawayen Kogi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)