Babbar hukumar dake lura da hada-hadar kasuwanni ta kasar Sin, ta ce an tsara wani shiri na shekaru 3, wanda zai mayar da hankali wajen inganta yanayin gajiyar masu sayayya a kasar, wanda za a fara aiwatarwa tun daga shekarar 2025 dake tafe da nufin bunkasa cinikayyar cikin gida.
Wasu alkaluman hukumar kididdigar kasar Sin ko NBS, sun nuna yadda cikin watanni 11 na farkon shekarar nan ta 2024, sashen cinikayyar kayayyaki daidai ya kai darajar kusan yuan tiriliyan 44.3, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 6.16, adadin da ya karu da kaso 3.5 bisa dari a shekara.
A daya bangaren kuma, darajar sashen cinikayyar kayayyaki ta yanar gizo, ya kai kusan yuan tiriliyan 14, adadin da shi ma ya karu da kaso 7.4 bisa dari. (Saminu Alhassan)