A ci gaba da kokarin da take yi na samar da ci gaba da bunkasar tattalin arziki ta hanyar noman zamani, Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar Jigawa wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin Sin, CAMC Engineering Co., Ltd. (CAMCE) da kuma Asusun bunkasa aikin gona na Nijeriya a hedkwatar kamfanin dake birnin Beijing na kasar Sin.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan kan harkokin yada labarai, Hamisu Mohammed G. Ya fitar a ranar Talata, 24 ga watan Disamba, 2024.
- Kakakin Majalisar Tarayya Da Mataimakinsa Sun Taya Kiristoci Murnar Bukukuwan Kirismeti
- An Kashe Mutane 14 A Wani Sabon Harin Filato
Wannan tsarin hadin gwiwa yana da nufin kawo sauyi a fannin noma na jihar Jigawa ta hanyar inganta samar da kayayyaki, sarrafawa, da kuma samar da cinikayya ga muhimman kayayyakin gona.
Taron rattaba hannu kan yarjejeniyar, wanda Gwamna Namadi ya jagoranta, ya samu sa hannun Hon. Muttaga Namadi, Kwamishinan Noma na Jihar Jigawa; Mohammed Abu Ibrahim, babban sakataren asusun bunkasa noma na kasa; da Mista Sun Jianshan, babban manajan kamfanin CAMC na sin.
Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Muttaga Namadi ya bayyana hadin gwiwar a matsayin wani yunkuri na gwamnatin jihar Jigawa na kawo sauyi a fannin noma a jihar.