Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar da rahoton jerin ƙasashen 10 da suka fi cin bashi a nahiyar Afirka, a lokacin da ƙasashen ke fama da matsanancin bashin da ya dabaibaye su.
Rahoton ya bayyana cewa, duk da ɗimbin bashin da Nijeriya ke karɓowa, ba ta cikin jerin ƙasashen da suka fi dogaro da lamuni daga IMF a Afirka.
- Sin Na Matukar Adawa Da Binciken Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Sana’o’in Na’urorin Lantarki Na Kasar Sin
- Sin Ta Sha Alwashin Karfafa Kare Muhallin Halittun Rawayen Kogi
Akwai ƙasashe 10 da suka yi fice wajen karɓar bashin IMF, galibi don cike gibin kasafin kuɗi da kuma magance matsalolin tattalin arziƙi.
Koyaushe, IMF na gindaya tsauraran sharuɗa, kamar cire tallafi, rage darajar kuɗaɗen ƙasa, da tsuke bakin aljihu kafin bayar da bashin.
Ga jerin ƙasashen 10 da suka fi cin bashi daga IMF:
1. Masar – Ta karbi bashin dala biliyan 9.45, tana cikin matsanancin hali na tattalin arziƙi.
2. Kenya – Ta karɓi dala biliyan 3.02 don bunƙasa tattalin arziƙi da magance matsalolin cikin gida.
3. Angola – Ta dogara kan dala biliyan 2.99 don farfaɗo da tattalin arziƙinta.
4. Ghana – Ta karɓi dala biliyan 2.25, tana fama da karyewar darajar kuɗi.
5. Ivory Coast – Dala biliyan 2.19 don aiwatar da tsare-tsaren ci gaba.
6. Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo – Ta amshi dala biliyan 1.6 don magance matsalolin tattalin arziƙi duk da arziƙin albarkatun ƙasa.
7. Habasha – Ta karɓi dala biliyan 1.31 don magance matsalolin tattalin arziƙi.
8. Afirka ta Kudu – Dala biliyan 1.14 don tunkarar matsalolin cikin gida.
9. Kamaru – Ta ciyo dala biliyan 1.13.
10. Senegal – Ta karɓi dala biliyan 1.11 bayan karɓar tsauraran sharuɗa na IMF.
Dogaron ƙasashen Afirka kan bashin IMF yana nuna karuwar matsalolin tattalin arziƙi, yayin da suke ƙoƙarin cike gibin kasafin kuɗi da cimma burin ci gaba mai ɗorewa.