Kakakin babbar majalisar dokokin kasar Sin ya bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta yi watsi da tunaninta na yakin cacar baka da son zuciya, da kuma kauce wa tanada munanan abubuwan da suka shafi kasar Sin a cikin dokar ba da iznin tsaron kasa (NDAA) na shekarar kasafin kudi ta 2025.
Kakakin kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Xu Dong, ya bayyana matukar rashin gamsuwar kasar Sin da kuma nuna adawa da munanan abubuwa da ke cikin dokar masu nufin illata kasar Sin. Yana mai bayyana cewa, majalisun dokokin Amurka sun amince da NDAA na shekarar kasafin kudi ta 2025, kuma shugaban kasar Joe Biden ya sanya hannu kan dokar,
Ya soki NDAA kan ci gaba da yada ikirarinta na “barazanar kasar Sin,” tana kuma ba da goyon bayan soja ga Taiwan, da dakile ci gaban kimiyya, fasaha da tattalin arziki na kasar Sin, tare da takaita muamalar tattalin arziki, cinikayya da jama’a tsakanin Sin da Amurka, da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da kuma kawo cikas ga ‘yancin kai, tsaro, da muradun ci gaban kasar Sin. (Mohammed Yahaya)