A yayin da ake shirin ban kwana da shekarar 2024, kasar Sin ta yi matukar rawar gani a fannin bunkasa fasahar sadarwa ta zamani, a yayin da ta zama kasa ta farko a duniya, wacce adadin kayayyakinta na intanet suka zarce yawan daukacin masu amfani da wayoyin salula a cikin kasa.
Zuwa cikar kwanakin da suka rage a shekarar, ana sa rai kayayyakin na intanet da suka kunshi na’urorin karbar sakonni da sarrafa su da aike su zuwa sassan da ake bukata su zarce biliyan 3, kamar yadda bayanan da aka fitar a yayin gudanar da taron intanet na duniya, a watan Nuwamban da ya shige suka nuna.
Tun a watan Yulin bana, adadin tasoshin sadarwar wayoyin salula sun riga sun kai miliyan 11.93 kasar, kana, alkaluma daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, watau MIIT sun nuna cewa, a karshen watan Nuwamba, yawan masu amfani da fasahar 5G ta wayoyin salula a kasar sun kai biliyan 1.002, inda wannan adadi ya nuna kashi 56 cikin dari na daukacin masu amfani da wayoyin salula da suke amfani da layukan kamfanonin sadarwar kasar Sin irin su: China Mobile, China Unicom, China Telecom, da kuma China Broadnet. Har ila yau, hakan ya nuna an samu karuwar masu amfani da fasahar ta 5G da kashi 9.4 cikin dari, idan aka kwatanta da na karshen bara.
Zuwa karshen watan Nuwamba, kasar Sin tana da adadin masu amfani da wayoyin salula a kalla biliyan 1.79, dake nuna an samu karin kimanin miliyan 46.82 idan aka kwatanta da na bara war haka.
Tun a farkon bana dai, alkaluman masana’antu sun nuna cewa, tasoshin 5G na kasar Sin, da suka kasance manyan wuraren sada wayoyi da intanet, sun kai fiye da kashi 60 cikin dari na daukacin adadin wadanda suke kasashen duniya, wanda yake nuna matsayin kasar na zama a kan gaba wajen samar da fasahar 5G a duniya.
An samu bunkasar amfani da fasahar 5G cikin hanzari ce bisa habaka samar da kayayyakin aiki a bangaren. Alkaluman ma’aikatar MIIT sun nuna kasar Sin ta samar da tasoshin fasahar 5G kimanin miliyan 4.2 zuwa karshen watan jiya, wanda ya nuna an samu karin kimanin 815,000 a kan na bara war haka.
Sakamakon kokarin da Sin take yi na habaka fasahar zamani ta fuskoki daban-daban, ana sa ran tattalin arzikin kasar a wannan bangaren kadai ya zarce yuan tiriliyan 70 (dala tiriliyan 9.84) saboda ci gaban da za a samu a bangaren zai rika karuwa da kashi 20 cikin dari. Yanzu haka akwai kamfanoni kusan miliyan daya da suka kimtsa tsaf domin zurfafa ci gaban kasar a bangaren tattalin arzikin fasahar zamani.
Kazalika, kasar ta kuma sha damarar samar da sabbin manyan harkokin intanet na cikin gida da wadanda za su zama na duniya guda 30 a shekarar 2025 mai kamawa. Wannan na daga cikin gudummawar da Sin za ta bayar ga kokarin da ake yi na ganin an samar da harkokin sadarwa a duniya masu hade da juna a kalla biliyan 25 a sabuwar shekarar ta 2025. (Abdulrazaq Yahuza Jere)