Dakarun Sojojin haɗin gwuiwa na atisayen haɗin kai sun samu nasarar daƙile wani hari da Boko Haram/ISWAP suka yi amfani da jirgin sama mai ɗauke da makami a Buni Gari, Jihar Yobe, a ranar Laraba. Wata majiyar Soja ta bayyana cewa, Sojojin sun gano jirgin mai dauke da roka yana tunkarar sansanin rundunar 27 Task Force Brigade da misalin ƙarfe 4:35 na yamma.
Bayab saurin ɗaukar mataki, Sojojin sun harbo jirgin kafin ya samu damar sakin rokar da ke jikin sa. An kuma tabbatar da cewa, rokar ta lalace ba tare da ta jawo asarar rai ko rauni ba, bayan da masana abubuwan fashewa (EOD) na Sojojin suka tarwatsa ta cikin nasara. Sojojin sun kuma tura wasu jiragen leƙen asiri domin bincikar yankin, amma ba a gano wata barazana ba.
- Sojojin Ruwan Sin Da Na Kasashen Yankin Tekun Guinea Za Su Tattauna Game Da Tsaron Teku
- Mayaƙan ISWAP Da Boko Haram 4 Sun Tuba Sun Miƙa Wuya A Borno
Wannan shi ne karo na biyu da aka samu rahoton amfani da jiragen sama maras matuƙi wajen kai hari a sansanin Sojojin.
A baya, Boko Haram/ISWAP sun yi irin wannan hari a Jihar Borno, wanda ya jikkata Sojoji biyar. Har yanzu babu wani rahoto daga hukumar hulɗa da Jama’a ta Sojoji.