Wasu kungiyoyin mata da matasa a jihar Bauchi sun yi gangami a ofishin Sanata Halliru Dauda Jika inda suke kiransa da ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP mai alamar kwando da kayan marmari domin samun zarafin fitowa takarar gwamnan Jihar Bauchi a 2023 da ke tafe.
Wakilinmu ya labarto cewa Sanata Halliru Dauda Jika dai shine ke wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a Majalisar Dattawa ya fito neman tikitin APC na kujerar gwamna amma Air Marshal Saddique Baba Abubakar ya kayar da shi a zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a kwanakin baya.
Da ya ke jawabi a wajen gangamin, Sadik Abdullahi Kobi, Shugaban kungiyar mata masu dogaro da kansu na jihar Bauchi, ya shaida cewar, babban burinsu shine Sanatan ya amince ya fito neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar NNPP domin cire musu kitse a wuta.
Ya ce: “Wannan dandanzon mata da matasa da ka gani sun fito ne domin yin kira ga Sanata Halliru Dauda Jika da ya fice daga jam’iyyar APC ya shiga jam’iyyar NNPP domin ya samu damar yin takarar gwamnan Jihar Bauchi a 2023.”
“Daman mun gargadi uwar jam’iyyar APC ta dauki tikitin neman takarar gwamna ta bai wa Sanata Jika saboda shi ne yake tare da mutane, shi ne yake mutunta mutane, shine ya san matsalolinsu, shine yake kawo cigaba ga kuma shine suke so, sabanin wanda aka zo aka kakaba mana da karfin tsiya. Don haka muke son ya bar jam’iyyar ya koma NNPP mu kuma muna tare da shi dari bisa dari.
“Don haka mu a matsayinmu na mata da matasa muna nuna wa Sanata Jika hanyar da ya dace na cewa ya zo ya bi abun da jama’a ke so. Abun da jama’a ke so kuma shine ya shiga NNPP ya mana takarar gwamna.”
Abdullahi Kobi ya bada tabbacin cewa muddin Jika ya amince ya fito neman takarar gwamna a NNPP tabbas jama’an jihar za su zabeshi domin sun amince da salon jagorancinsa da kyautata musu, “al’umma ke kawo mutum musamman mata. Ka ga kuwa al’ummar ne suka ce lallai ya zo ya musu takara. Don haka muna da kyakkyawar fatan shine zai yi nasara a babban zaben 2023.”
A bangarenta, Malama Saliha Abubakar ta bayyana cewar a shirye suke su shiga lungu da sako domin nema wa Sanata Jika kuri’u, tana mai cewa sun amince da cewa ya fi kowani dan takara dacewar da zai iya jagorantar jihar Bauchi yadda ya kamata.
“Mu iyaye mata mune mu kan irin halin da muke cikin a hali yanzu. Don haka muna rokon ya amsa kiran mu ya koma NNPP domin mu mara masa baya.”
Da ya ke amsar bukatun kungiyoyin a madadin Sanatan, Haruna Muhammad daya daga cikin hadiman Sanata Jika, ya gode wa kungiyoyin bisa nuna damuwa da soyayya ga Sanata Halliru Dauda Jika ya kuma ba su tabbacin cewa za su yi zama na musamman kan wannan bukatar tare da daukan matakin da ya dace domin cigaban jihar Bauchi.
Ya ce, tabbas Sanata Jika na yi ne don al’umma kuma zai sauraro bukatunsu tare da yin abun da dace. Ya ba su tabbacin cewa da izinin Allah Sanata Jika zai yi takarar gwamna a 2023.