Yakin Gaza ya haifar da Kirismeti lami a Bethlehem, karo na biyu a jere.
Ba a gudanar da bukukuwa ba a dandalin cocin da aka gina a wurin da aka haifi Yesu Almasihu, ba kuma a kunna kyandura ko ajiye bishiyar Kirsimeti ba.
- Muhammad Salah:Â Gwarzon Afirka A Firimiyar Ingila
- Fiye Da Kaso 80 Na Kamfanonin Sin Sun Fadada Zuba Jari A Waje A 2024
Wakiliyar BBC ta ce an dai hango yara suna tattaki dauke da rubutu a takardu da ke kira da a kawo karshen yakin Gaza.
Babban limamin mabiya Katholika a Birnin Kudus, ya ce duk da halin tabarbarewa da Gaza ke ciki, ya umarci jama’a su kasance da kwarin gwiwa da kyakyawan fata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp