Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da cewa, ta mayar da ‘yan gudun hijira su 12,000 zuwa matsugunan da ke a yankin Shimfida a karamar hukumar Jibia ciki har da mata da yara.
Shugaban karamar hukumar na Jibia Bishir Sabi ne ya sanar da hakan, inda ya ce, al’ummar sun kaurace wa yankin ne a ranar 10 ga watan Maris biyo bayan kwashe sojojin da aka girke a yankin saboda hare -haren ‘yan bindiga, inda hakan ya janyo mutuwar wasu mutane da dama.
Kafin dawowar ‘yan gudun hijira sama da 6,000 gwamnatin jihar ta samar masu da matsuguni na wucin gadi a makarantar sakandare ta gwamnati da ke a Jibia, inda kuma wasun su, suka arce zuwa jamhuriyar Nijar wadanda suma ana dawo da su zuwa Jibia.
Ya ce, kafin a dawo da su, gwamna Masari ya tattauna da shugaba Muhammadu Buhari, inda shugaban ya bayar da tabbacin samar da tsaro a karamar hukumar.
Shugaban ya kara da cewa, an maido da su ne ganin cewa, daminar bana ta kankama, kuma muna son su koma gonakan su domin su ci gaba da yin noma.
Bashir ya ce, tun da farko gwamnatin jihar ta fitar da Naira miliyan 88.6, inda gwamnatin ta kara amince wa da a fitar da wasu karin Naira miliyan 18 domin a samar da magunguna da sauran kaya ga ‘yan gudun hijirar da kuma wasu ma’aurata masu yin aiki na musamman a yankin.