Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure, sabon Mai Bashi Shawara Kan Ayyuka, wanda ya rasu a ranar Laraba a ƙasar Masar, kwana ɗaya bayan rantsar da shi.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.
- Yarinyar Da Ake Zargi Da Zuba Wa Mijinta Da Abokansa Guba A Abinci, Ta Amsa Laifinta A Kotu
- Shugaba Xi Ya Ba Da Umarnin Aiwatar Da Dukkanin Matakan Da Suka Wajaba Na Ceto Biyowa Bayan Girgizar Kasa A Xizang
Gwamnan yaba wa jajircewa da ƙwarewar Injiniya Bunkure, wanda ake sa ran zai bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.
Marigayi Injiniya Bunkure an san shi da ƙwarewa a fannin kayayyakin more rayuwa, wanda hakan ya sa gwamnati ta ba shi amana.
A cewar gwamnan rasuwarsa ta bar babban giɓi a zukatan mutane.
Tuni ‘yan uwa da abokan arziki suks shiga yin ta’aziyya daga sassa daban-daban, ciki har da ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin, ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jure wannan rashi.