A cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar na maraba da sabuwar shekarar nan ta 2025, ya jaddada aniyar kasarsa ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya, don kara inganta koyi da juna tsakanin mabanbantan aladu da wayewar kai. Wadannan kalamai na shugaba Xi, shaida ce dake kara fito da shirin kasar Sin fili, a fannin amfani da kwarewa, da hangen nesa wajen ingiza kyakkyawan yanayin zaman tare tsakanin wayewar kai daban daban, da ma kwazon kasar na sauke nauyin dake wuyanta, na yayata ci gaban wayewar kan daukacin bil adama.
Ko shakka babu duniyar yau tana cike da sabbin yanayi na tangal-tangal, da sauye-sauye, yayin da karin kalubale ke bullowar duniya. Kuma magance manyan kalubalen dake addabar dan adam na bukatar wanzar da zaman lafiya, da zaman jiyuwa tsakanin mabanbantan wayewar kai.
- Xi Ya Jagoranci Taron Shugabannin JKS Game Da Ayyukan Tallafin Jin Kai Bayan Aukuwar Girgizar Kasa A Xizang
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Lashi Takobin Karfafa Hadin Gwiwa Da Afirka
A gani na, yayin da wasu sassan kasa da kasa ke aiwatar da matakan ware kai, da baiwa kasuwa kariya, da nuna fifiko, kasar Sin a nata bangare ta rungumi matakai masu kyau na sada zumunta da sauran sassa, ta hanyar musaya, da koyi da juna, matakan da za su baiwa sassan kasa da kasa damar amfana daga wayewar kan kasar Sin, wanda ya samo asali daga tarihinta na sama da shekaru 5,000.
Sanin kowa ne cewa cin gajiyar wayewar kai, da bunkasa rayuwar dan adam ba za su samu ba, muddin ba a cimma matsaya, da budewa juna kofa, da yin tafiya tare, da musaya, da koyi da juna tsakanin mabambantan wayewar kai ba. Kara tattaunawa zai rage fito na fito, yayin da yin tafiya tare zai rage rashin fahimtar juna. Hakan ne ma ya sa a watan Yunin shekarar 2024 da ta gabata, babban taron MDD karo na 78, da babban rinjaye ya amince da kudurin da kasar Sin ta gabatar, na kafa ranar kasa da kasa ta tattaunawa tsakanin mabanbantan wayewar kai. Wani mataki da a gani na ya zama misali, na yadda kasar ta Sin ke gabatarwa duniya dabarun warware wasu manyan matsaloli, musamman a wannan gaba da nufin kawar da kyamar juna, da ingiza fahimtar juna, da kyautata amincewa juna tsakanin sassan kasa da kasa.
A daya bangaren kuma, cimma burin zamanantarwa muhimmin batu ne mai nasaba da fatan bunkasa wayewar kan dan adam. Zamanantarwa ba aiki ne da ya shafi wasu tsirarun kasashe kalilan ba, kana ba zai yiwu ya zamo salo daya tak da za a kwafa daga wani yanki a kai wani yanki ba. A tafiyar zamanantarwa, kasar Sin ta yi imani da yin tafiya, da aiki tare da sauran kasashe, ta yadda za su hada karfi da karfe wajen yin musayar kwarewa, har a kai ga gina kasashe daban daban, da gina alummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya, wadda daukacin bil adama zai yi alfahari da ita.(Saminu Alhassan)