Yau Alhamis 9 ga wannan wata, alkaluman kididdiga game da hauhawar farashin kayayyaki ko CPI a takaice a shekarar 2024 da hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS ta fitar sun karu da kaso 0.2 bisa dari a kan na makamancin lokacin shekarar 2023. An lura cewa, a watan Disamban bara, alkaluman CPI na kasar Sin sun karu da kaso 0.1 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2023.
A sa’i daya kuma, alkaluman kididdigar farashin kayayyakin da ake sayarwa a kofar masana’antu ko PPI a takaice a kasar Sin a watan Disamban bara sun ragu da kaso 2.3 bisa dari a kan na makamancin lokacin shekarar 2023. Amma a watan Nuwamban bara, alkaluman sun ragu da kaso 2.5 bisa dari, sakamakon tafiyar hawainiyar samar da kayayyaki da sauyawar farashin kayayyaki a kasuwar kasa da kasa. (Mai fassara: Jamila)