Zaman lafiya shi ne ginshikin duk wata rayuwa bama ace irin rayuwa ta iyali wadda idan aka yi sa a al’amura suna tafiya kamar yadda ya dace, shi kan shi ko su kansu masu irin wadannan halayen sai sun fi jin dadin rayuwar aure da matansu.Awai wani gidan da na sani ba fada mani aka yi ba,domin shi Maigidan abinda yake yi shi ne idan dan wancan matar ya isa ‘yaye sai ya kai ma kishiyarta ko abokiyar zama ta daya dakin.
Haka yake tafiyar da harkokin gidansa,wani yaron ma bai sanin mahaifiyarsa sai ranar daya kammala Jami’a, ko kammala yi ma kasa hidima abinda aka fi sani da Bautar kasa.Ita kuma ‘ya macen ba a nuna mata mahaifiyarta sai ranar da aka daura mata aure.
- Ingancin Makarantu Masu Zaman Kansu Ya Tabarbare
- Waiwayen Tsarin Hulda Da ƙasashen Waje Na Nijeriya A Matsayin Mafita
Yana kuma yin hakan ne domin ya samu hadin kan matan nasa wanda kuma haka abin ya kasance har bayan rayuwarsa.Zai kuma yi wuya ka shiga gida ka ji ana ta musanyar maganar da bata kamata ba tsakanin matansa.
Amma wasu Mazan ko Magidanta halayensu abin sai dai ayi sha’ani wai an cuci na kauye, da zarar sun yi wani sabon aure sai su canza yadda suke tafiyar da al’amuransu.Matar da Amarya ta tarar wato Uwargida sai a rika ci mata mutunci ta hanyar yin abubuwan da basu kamata ba, Wata rashin jituwa ko tashe- tashen hankula tsakanin matansu, sune suke kasancewar mafarin faruwar al’amarin.
Daga karshe dai wani har sai ya cimma burinsa na korar ita Uwargidan ta halayen shi daya canza, in aka samu wadda bata da hakuri koda kuwa ba sakinta yayi babata iya tsayawa da cigaba da ganin wulakanci.Bai ma tsayawa sai ta yi ma shi wani abinda bai dace ba tukuna hakanan sai ya dauki karan tsana ya rika nuna ta da shi. Babbar illar raba kan mata da wasu Magidanta suke yi ba karama bace wadda kuma take kawo matsalar da zata iya shafar rayuwar duk wadanda suke gidan baki daya. Domin kuwa matukar shi Maigidan da ya tara dukkan matanda suke gidan bai gyara halin sa na yin abubuwan da basu dace ba, don kawai ya farantawa ita Amaryar zuciyarta,to abin fa daga karshe ba zai haifar da da mai ido ba.Idan aka yi rashin sa’a har ita Uwragidan ta fita a sanadiyar ko shi Mijin ya sake ta,ko kuma taga cewar ba zata iya jure ma zaman gidan ba, a irin wannan yanayin ta yi tafiyarta.
A karo na farko matsalar da shi Maigidan zai fara fuskanta ko su ‘ya’yanta ita ce ta kula da tarbiyyarsu kamar yadda mahaifiyar su take yi masu,saboda ba dole bane kishoyinta ko kishiyarta su yi ma ‘ya’yan tarbiyyar yadda mahaifiyarsu take yi masu data dace.
Wannan ya nuna ke nan maganar gaskiyar ba ance wasu ba za su iya tarbiyyar ‘ya’yan wasu ba ne,amma abin kallo anan shi ne,wasu da biyu ne da gangan za su yi ta yi masu ingiza mai kantu ruwa suna sa su hanya ko hanyoyin da tarbiyarsu za ta gurvace wanda abin daga karshe su kasa rashin amfanar su kansu da ma masu hulda da su kai tsaye ko a kaikaice.
Shi ma mahaifin ko Maigidan da zai cigaba da aiwatar da irin yara tsanar ko kiyayyar da yake nunuwa nahaifiyar su ‘ya’yan zuwa gare su,duk wani abinda da suka yi ko dai dai ko akasin haka ba zai ce masu uffan ba, sais a masu idanu bama kamar idan aka yi rashin sa’a suna kanana.
Wannan ba karamar illa bace ta kan kuma faru a gidaje daban- daban sa salon halayen Maigida wanda ya kasance mai al’adarnan ta Auri–Saki. Saboda kuwa tana iya shafar al’ummar gidan gaba daya. Zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kan yi wuya a ire-iren wadannan gidajen, ko Unguwa da ma Gari baki ɗaya.